JARUMI a Kannywood, Habibu Yaro Haruna, ya ce a cikin harkar fim a yanzu ba a neman ƙwarewa ko cancanta idan an tashi yin aikin fim, don haka ne a matsaloli su ka dabaibaye harkar.
Jarumin, wanda darakta ne kuma furodusa,
ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim kan halin da masana’antar ta samu kan ta a yau.
Malam Habibu ya ce, “Ni dai a masana’antar nan ta Kannywood ba yaro ba ne a game da ita harkar fim ɗin, domin ban ce a shekaru ba, a daɗewa a cikin harkar a yanzu ba za a samu mutane ashirin da za a ce sun girme ni a cikin harkar fim ba, don na shigo harkar fim tun ba na iya bambancewa tsakanin namiji da mace.
“Ko da ka ji ana cewa Habibu Yaro ɗin nan, to a cikin harkar fim na samu sunan yaro saboda ƙanƙanta ta. Kuma alhamdu lillahi a tsawon zama na a cikin harkar fim tun ina a matsayin ɗan aike na zama jarumi, na zama furodusa, na zama darakta, na zama mai ɗaukar hoto, don haka duk wani aiki na harkar fim na yi shi.”
Ya ci gaba da cewa, “Ni sanin da na yi wa ita harkar fim, labari shi ne ya ke kiran jarumi, idan labari ya dace da jarumi sai a kira shi ya yi aiki daidai da matsayin sa. To amma a yanzu mun tsallako wani lokacin da kusanci ko alaƙar ka da mutum ko don wata biyan buƙata, ita ce ta ke taka rawa, ba wai cancanta ba. Don magana ta gaskiya a yanzu a cikin fim goma da za ka gani, to ɗaya ne za ka ga an saka shi domin ya cancanta.
“To mu kuma mun shigo wannan masana’antar ne saboda mu na da tunanin cewar ta kasance sana’a. Wannan ya sa da mu ka ga ita masana’antar ta na da faɗin gaske wadda idan ka koma to za ka ci abinci a cikin ta, duk da ya ke an fi ganin jarumai su kuma zamani a koro da ya zama ba a maganar cancanta, sai dai maganar aboki ko ƙane ko ɗan’uwa su ne ake iya sakawa.
“Amma dai alhamdu lillahi don abin da mu ka iya dangane da aktin, to shi ba ya guduwa, don baiwa ce sai ma dai wani abin ya ƙaru. Wannan ya sa na ɗan ɗaga ƙafa a maganar fitowa a cikin fim duk da cewar akwai wasu dalilai da yawa wanda ba sai na fito na faɗa wa duniya ba.
“Amma dai abu mafi girma shi ne ba a bari labari ya kira jarumi. Kuma in dai son rai zai sa a kira jarumi, to ba na jin mu za a yi da mu, amma dai ba don ba mu iya ba, saboda haka sai na koma gefe ina yin wasu harkoki na da ya ke shi aktin ba shi kaɗai na iya ba, don akwai abubuwa da yawa wanda tun a can baya su iyayen gidan mu sun koya mana kuma ya zame mana sana’a, saboda haka ban samu damuwa ba don na daina fitowa a finafinai na wannan masana’antar.
“Don rabon da na fito a wani fim na wannan masana’antar tun wani fim ‘Kuyanga’.
“Kuma na san za ka tambaye ni ko na fito a ‘Kwana Casa’in’. Amma dai zan iya cewa ban fito ba, don wataƙila kai ka iya gane ni, amma dai duniya ba ta san waye ni ba, don ba a ba ni rol ɗin da za a iya gane ni ba, sannan shi daraktan bai iya bayyana ni ba yadda za a san ni a matsayin jarumi ba, don haka sai na ke ji ba fim na shiga ba, kawai ɗan yawo na je yi. Amma dai ina sa ran nan da 2024 zan ita dawowa fim.
Domin akwai wani fim nawa da na ke rubutun labarin kuma ni zan shirya kaya na, kuma in Allah ya yarda ina son na ga na gabatar da shi.
“Don haka babban buri na shi ne a samu jagorancin da ita masana’antar za ta tsaya da ƙafar ta. Don haka ina fatan Allah ya ba shugabancin da zai saita masana’antar, kuma mu na fatan mu samu gwamnatin da za ta samar da cigaba kuma ta yarda wannan masana’antar ta na ɗaya daga cikin masana’antun da za su samar wa matasa da ayyukan yi a ƙasar nan.”