FITACCEN jarumin barkwanci, Ali Artwork (Maɗagwal) ya bayyana cewa Adam A. Zango ya daɗe ya na yaudarar ‘yanmata, ba Ummi Rahab ce farau ba.
Haka kuma ya ce yanzu duniya ta gane cewa ashe shi Zango shi ne butulu, ba Rahab ba.
Maɗagwal ya faɗi haka ne a wani rubutu da ya yi bayan ya tura wani bayanin bidiyo na mariƙin Rahab, wato Yasir M. Ahmad.
A ‘yan kwanakin nan dai ana ta ce-ce-ku-ce a tsakanin jarumi Adam Zango da magoya bayan sa a ɓangare ɗaya da kuma Rahab da magoya bayan ta a ɗaya ɓangaren.
A hirarraki biyu da aka yi da shi ta hanyar bidiyo, waɗanda aka watsa ta hanyar soshiyal midiya, Zango ya bayyana cewa ya raba hanya da jarumar ne lokacin da ta ƙi bin turbar tarbiyya da ya ɗora ta a kai, sannan su kuma magoya bayan sa sun bayyana yarinyar a matsayin butulu wadda ta juya masa baya ta koma wajen maƙiyan sa.
Maɗagwal, wanda aminin Yasir ne, ya wallafa wani bidiyo inda Yasir ɗin ya yi wa duniya bayani kan abin da ya kira gaskiyar abin da ya faru tsakanin jarumar da jarumin.
A ƙasan bidiyon, Maɗagwal ya yi bayani mai kaushi inda ya ce yanzu gaskiya ta bayyana daga bayanin da Yasir ya yi.
Ya fara da cewa, “Inna lillahi wa inna ilaihir raju’un! To jama’a kun dai ji gaskiyar magana daga bakin ɗan’uwan Ummi Rahab, wato Yasir Rahab. Allah ya kyauta.”
Ya ci gaba da cewa, “Da ma Musulunci ya ce duk abin da za kai, ka yi bincike, kar ka yi saurin yanke wa ɓangare ɗaya hukunci. Shi ya sa mu ka ce jama’a ku yi bincike a kan wannan lamari; ita fa gaskiya guda ɗaya ce, daga ƙin ta sai ɓata. Allah ka dauwamar da mu a kan tafarkin gaskiya.”

Ya ƙara da cewa, “Allah sarki Ummi Rahab! An so a yi miki shigo-shigo ba zurfi, amma Allah ya tsare ki, shi ne ake son a fake da kin yi butulci ko kuma ba kya jin magana.”
Ya ce da man Zango ya saba irin wannan ɓatawar da yaran kamfanin sa, musamman matan.
Ya ce, “Jama’a ina so ku sani, wannan mutumin ba a kan wannan yarinyar ya fara yaudara ba. Ya yi wa mata da dama haka. Don haka in ba za ku manta ba, wannan mutumin ya yi rigima da mata da dama a wannan masana’anta, daga ƙarshe sai ya ce sun masa butulci saboda kawai ya nema bai samu ba.
“Daga ƙarshe sai ya yi amfani da makafin masoyan sa ta ƙarfin tsiya sai sun dawo mai da yarinyar gurin sa don kawai ya cutar musu da ‘yar marainiyar Allah don ya cimma wata mummunar manufar sa.
“Ku kuma masoyan sa ba ku san me ya ke faruwa ba sai ku yi ta goya masa baya ya na jin daɗi.
“Yanzu kai da ƙanwar ka ko ‘yar’uwar ka aka yi wa haka, za ka ji daɗi? Kawai a zo soshiyal midiya, ba ta san hawa ba ba ta san sauka ba, a ce ta yi butulci? A sa mutane su yi ta zagin ta da la’anta, ba ta ji ba ba ta gani ba, ‘yar ƙaramar yarinya da ba ta san komai ba wai a ce ta bijire!
“Hakan na nufin ta tafi karuwanci kenan, alhali kuma yarinya babu inda ta ke zuwa daga gida sai gun aikin ta? Wannan ba daidai ba ne, a ɓata sunan ‘yar da duk mai son ta ya aure ta zai fara mata kallon ta na zuwa yawon bariki.”
Da ya juya kan Zango, sai ya ce, “Ka ce za ka aure ta, ka gudu ka ƙi komawa. Wanda su ke son ta tsakani da Allah ka sa musu shakku a kan ta. Shi kenan ka na son ka hana ta aure ko? Ƙaramar yarinya a sa mutane su tsane ta babu gaira babu dalili.”
A cewar Ali Artwork, “Ya kamata ‘yan’uwa mu ji tsoron Allah, mu guji yaɗa ji-ta-ji-ta. Allah ma ya hana haka.

“Kuma in-sha Allah wannan yarinyar za mu ci gaba da yi mata addu’a.”
A ƙarshe, jarumin ya yi addu’a kamar haka: “In-sha Allah ba zai ƙara yi wa wata ‘ya mace haka ba. Don haka mu na ƙara addu’ar Allah ya ƙara tsare miki mutuncin ki, Ummi Rahab. Allah ya ba ki miji nagari ki yi auren ki ki zauna.”