• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

'Ta samu karɓuwar Kannywood, kuma za ta yi tasiri'

by ABBA MUHAMMAD
March 1, 2025
in Tattaunawa
0
Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

Alhaji Adamu Muhammad Bello (Ability), Shugaban Network for Kannywood Guilds and Associations (NEKAGA)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ALHAJI Adamu Muhammad Bello (Ability) yana ɗaya daga cikin mutum biyu da suka yi takarar zama Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) da ya gudana a ranar 18 ga Janairu, 2025 a Lafiya, Jihar Nassarawa, sai Alhaji Maikuɗi Umar (Cashman) ya lashe zaɓen.

Kwatsam, sai kuma aka ji Ability da gungun wasu ‘yan fim sun kafa sabuwar ƙungiya mai suna Network for Kannywood Guilds and Associations (NEKAGA). A yanzu haka ƙungiyar ta zagaye dukkan jihohin Arewa tare da samun haɗin gwiwar wasu daga cikin ƙungiyoyin Kannywood guda bakwai.

Mujallar Fim nemi Ability domin zantawa da shi game da kafa wannan sabuwar ƙungiya, wadda wasu ke tunanin cewa an kafa ta ne saboda ya rasa kujerar shugabancin MOPPAN, aka yi wa MOPPAN kishiya.

Ability ya feɗe mana biri har wutsiya game da kafa ƙungiyar, kamar haka:

FIM: Menene maƙasudin kafa ƙungiyar Network for Kannywood Guilds and Associations (NKGA)?

ABILITY: To, ita sai wannan ƙungiya, dalilin kafa ta, kai ɗin nan da duk wani da ke harkar finafinai a arewacin Nijeriya zai yarda da cewa harkar shirya finafinai na Kannywood yana cikin garari, yana cikin takaici da baƙin ciki. Domin yau in ba sa’a ba, ba za ka zuba kuɗin ka ka yi fim, ba maganar riba ake yi ba, ka fitar da kuɗin ma, saboda tsarin kasuwancin ya canza, kuma tsarin yadda ake saida finafinan ya canza.

Ina so in sanar da kai akwai manyan furodusoshi – ba sai na kira maka suna ba – suna da finafinai a ƙasa, amma wallahi sun rasa yadda za a yi su fitar da su su sayar ta yadda za su samu kuɗaɗen su, akwai su da yawa.

To, Abba, dole dai mu duba wannan sana’ar, riba ta hanya biyu ne zuwa uku. In kuma aka ce duk an rasa waɗannan hanyoyin, sai an zauna kenan an sune shi. Ɗaya kenan.

Na biyu, yadda ita kan ta sana’ar ke tafiya a Arewa da kuma yadda su masu harkar shirya finafinan suke tafiyar da sana’ar shi kan shi abu ne ba wanda yake da daɗi ko ya dace ba. Na biyu kenan.

Na uku, ita kan ta gwamnati yanzu abubuwan ma ta sake shi ta yadda ba kamar yadda yake a da ba. Don haka muna buƙatar a ce an samu wani yanayi. Duk waɗannan yanayi za a yi abin da za a kawo sauƙi ko a gyara ko a tsaftace su ko kuma a tantance ta yadda za a cimma nasara.

Amma tsarin da muke da shi a yanzu, ba za mu iya cimma wannan nasara ba, gaskiya. Shi ya sa muka ga cewa akwai buƙatar a samar da wani yanayi da zai ba da gudunmawa ga sauran ƙungiyoyi da ke cikin wannan masana’anta, domin a yi taron dangi a ga yadda za a fitar da jaki daga cikin duma.

Kuma wallahi, ina so ka sani, wannan ƙungiya ba yau aka fara tunanin kafa ta ba. Ta daɗe ana tattaunawa a tsakanin juna haka da sauran mutane a ga ya za a yi a kawo mafita. Wanna shi ne kaɗan daga cikin dalilin da ya sa aka kafa wannan ƙungiya.

A ɓangare na biyu, in ka lura da yadda ‘yan fim suke, har yanzu a shekarun da muke fiye da shekara ashirin da biyar, har yanzu in ka lura finafinan mu ba za ka iya haɗa su da finafinai na ƙasashen da suka ci gaba ba saboda ba mu da ƙarfin jari, ba mu da kayan aiki, ba mu da ƙarfin ilimi na zamani.

Don haka muna so mu samu tallafi daga wuraren da aka ci gaba. Amma duk wannan ba za ka samu ba in ba kana da tsayayyun shugabanni ba, waɗanda suka san halin da harkar ke ciki, waɗanda suka san ina za a je a nemo waɗannan taimakon domin a bunƙasa harkar.

A ɓangare na uku, in ka lura, a ƙungiyoyin da muke da su, a matsayin ƙungiyoyi na ƙwato haƙƙin, ƙungiyoyi na taimakon masu sana’ar, yanzu su kan su sun shiga cikin wani hali na ni-‘ya-su. Muna da ƙungiyoyi da yawa na masu shirya finafinai a arewacin Nijeriya, amma yau za ka iske ko wadda take da rai ɗin ma, mutu-kwakwai-rai-kwakwai ne.

Abubuwan da duk ya kamata ta yi, gaskiya, ita kan ta ta gaza, ko don wajen rashin kuɗi ko rashin tsayayyu waɗanda suka san harkar ko kuma rashin ƙwararru da suke da jajircewa, suka san harkar finafinan, suka san yadda za a taimaka.

Waɗannan su ne matsalolin da suka sa muka ga cewa akwai buƙatar a sake kafa wata ƙungiya ko a samo wani yanayi da za a samu wata ƙungiya da za ta ba da gudunmawa domin a cimma nasarar ceto wannan masana’anta daga cikin halin ni-‘ya-su.

FIM: A taƙaice, menene manufofin ƙungiyar?

ABILITY: Manufofin ƙungiyar suna da yawa gaskiya. Na farko dai manufar mu shi ne, idan Allah ya ara mana lokaci, ya ba mu dama, mu sami mafita ga wannan sana’a ta yadda za a samu ɗaukaka, a samu cigaba, kuma cigaba ya zama mai ɗorewa. Wannan shi ne manufar mu na farko. Manufar mu na biyu shi ne dole – ko mun ƙi, ko mun so – sai mun shiga cikin gwamnati, domin akwai damarmaki da gwamnati ke kawowa waɗanda za su taimaka wa masu shirya finafinai da masu ɗaukar nauyi da sauran su, ta hanyar ba da rancen kuɗi, tallafi da kuma taimakawa wajen samun ilimin sana’ar ta hanyar zamani.

To, muna da manufar in Allah ya ba mu dama ƙungiyar nan ta kafu ta lungu da saƙo, domin nemo irin wannan damar, domin taimaka wa kan mu mu da muke wannan sana’a.

Sannan manufa ta uku, za ka yarda da ni, yau ba a iya tantance ɗan fim da ɗan TikTok, kowa an taru an zama ɗaya. Ya kamata a ce ɗan fim ya bambanta da ɗan TikTok. Ya kamata a ce ɗan fim ya zama mutum ne kamilalle, mutum ne mai mutunci, mutum ne mai koyar da tarbiyya, mutum ne mai ba da gudunmawa domin cimma nasara ga al’adu, domin kawo wa al’adu cigaba da ɗabi’un mu.

Ba wai kawai ɗan fim ya zama wanda ake misali da shi a matsayin mara kunya ko ɗan iska ko mara tarbiyya ba. Muna da manufa, mu zauna da masu wannan sana’a, mu tantance, mu zauna da su mu yi wa juna faɗa, mu yi wa juna nasiha, mu samu yanayi da za mu tsaftace sana’ar nan, domin sana’ar nan ta ci gaba da zama mai daraja, sannan mai ƙima.

Waɗannan suna daga cikin manufofin da muke so in Allah ya yarda mu samu dama da za mu taimaka wa wannan sana’a.

FIM: Ta ya ƙungiyar za ta yi gogayya da sauran ƙungiyoyin masana’antar?

ABILITY: To, ai tun a yanzu ma ƙungiyar ta fara bambanta da sauran. Dalilan su ne, ƙungiyoyi na masu wannan sana’a, kusan ƙungiya shida ko bakwai ne suka taru suka dunƙule suka zama wannan ƙungiyar guda ɗaya.

To, tun daga lokacin da aka ce ga ƙungiyoyi sun haɗu sun dunƙule, sun fitar da ƙungiya guda ɗaya, kai ka tabbatar da wannan ƙungiyar za ta yi tasiri. Babu faɗa kenan, babu ƙyashi, da sauran su. Ƙungiyoyin da ake taƙama da su ne suka zo suka haɗu suka dunƙule suka fitar da wannan ƙungiyar ƙwaya ɗaya.

Na biyu, sana’o’in da mu ke da shi a industiri, misali ƙungiyar ‘yan wasa, ƙungiyar furodusoshi, ƙungiyar daraktoci, ƙungiyar editoci su ne suka sake haɗuwa, suka haɗu da sauran ƙungiyoyin suka dunƙule suka shiga cikin wannan ƙungiya da muka kafa.

Ka ga tasirin ta ya bambanta da sauran ƙungiyoyin. In fact, ai yanzu babu sauran wata kungiya da ta fi wannan tunda ‘ya’yan ƙungiyoyin ne suka haɗu suka fitar da ƙungiya guda ɗaya.

FIM: Wasu na ganin cewa saboda an kada kai a zaɓen MOPPAN da ya gabata ne ya sa ka kafa wannan ƙungiyar. Me za ka ce?

ABILITY: A gani na, duk waɗanda suka faɗi wannan, sun faɗi son ran su ne. Domin lokacin da na fito takara, an tambaye ni dalilin da ya sa na fito takara. Da farko ban fito takarar nan ni da kai na ba, mutane suka taru, har gida na suka zo, suka nemi in fito takarar nan saboda la’akari da ilimi, ƙwarewa da basira da nake da su a wannan sana’ar, suka nemi in fito saboda suna da yaƙini da tabbacin ina da gudunmawar da zan iya bayarwa. Tun ina cewa a’a har na zo na yarda, har na bi.

To, wannan ƙwarewa da ilimin da Allah ya ba ni na wannan sana’ar, shi ya sa sai na ga ya kamata, tunda mutane suna so su amfana da ilimi na da ƙwarewa ta, sai na ce bari in ba da gudunmawa.

To amma kai kana naka ne, Allah yana nashi. Duk yadda muka yi ƙoƙarin mu nuna wa mutane muna da gudunmawar da za mu iya bayarwa, su ba su ga wannan gudunmawar ba, don haka ba su zaɓe mu ba.

Amma still muna da tunani akwai yanayi da za mu sake nunawa don mutane su fahimci wannan. Na faɗa maka wannan tsarin an faro shi tun ba yau ba, tun kafin a fara tunanin zaɓen MOPPAN wannan tunanin yake, zai kau shekara biyu ko uku da aka fara tunanin a fitar da A’i daga Rogo ko a fitar da jaki daga cikin duma.

FIM: ‘Yan Kannywood sun karɓi ƙungiyar?

ABILITY: Ƙwarai da gaske. Ai yanzu in ka ga ‘ya’yan ƙungiyar, sai abin ya ba ka mamaki. Bari in faɗa maka, duk wani wanda ake jin shi a Jihar Kano ko Jihar Kaduna ko sauran jihohi arewacin Nijeriya duk yana cikin wannan ƙungiyar.

A yanzu haka muna da jiha kusan goma sha biyar a cikin jihohi sha tara da muke da su a arewacin Nijeriya. Har ma mun yi nisa wurin kafa shugabanni na jihohi. Wannan shi zai nuna maka cewa ‘yan Kannywood sun karɓi wannan ƙungiya hannu biyu.

FIM: Ya kake kallon wannan ƙungiya a nan gaba?

ABILITY: Wannan ya danganta da yadda shugabanni suka tafiyar da ita. Yanzu ana ɗora ta a turba ta gaskiya, in-sha Allah sai ta yi tasiri, ta kuma daɗe ana fafatawa da ita, kuma za ta ba da gudunmawa ga masu sana’ar nan ta ko wane fanni. Don haka ina yi wa wannan ƙungiya kyakkyawan zaton alkhairi, dacewa, nasara da cigaba a nan gaba in-sha Allahu.

FIM: An yi mata rajista?

ABILITY: E, gaskiya mun yi nisa wurin yi wa ƙungiyar rajista. Sunan ta dai an karɓa, shugabannin ta da tsare-tsaren ta duk an karɓa, abin da ya rage in-sha Allahu muna jira mu karɓi satifiket ne.

FIM: Madalla. Muna godiya ƙwarai da gaske.

ABILITY: Ni ma ma gode, Malam Abba.

Loading

Tags: Adamu Bello AbilityMOPPANNetwork for Kannywood Guilds and Associations (NEKAGA)
Previous Post

MOPPAN ta nemi haɗin gwiwa da kuma agajin Jakaden Philippines

Next Post

Sakamakon ƙazafi, MOPPAN ta maka ɗan TikTok, Ahmed Pasali a kotu

Related Posts

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano
Tattaunawa

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

June 30, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV
Tattaunawa

Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV

February 14, 2024
Next Post
Sakamakon ƙazafi, MOPPAN ta maka ɗan TikTok, Ahmed Pasali a kotu

Sakamakon ƙazafi, MOPPAN ta maka ɗan TikTok, Ahmed Pasali a kotu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!