FITACCIYAR jarumar Kannywood, Ummi Ibrahim (Zee-Zee), ta bayyana cewa ita dai ba ta ga cikar imani a wajen malaman Musulunci na Nijeriya ba, domin kuwa babu wani daga cikin su da ya kira ta ya yi mata nasiha a kan iƙirarin kashe kan ta da ta ce za ta yi kwanan baya, maimakon haka sai tsina da zagi.
Zee-Zee ta bayyana haka ne a wani saƙo da ta tura a Instagram a yau bayan ziyarar da ta kai wa Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad, bisa gayyatar ita kwamishinar.
Ta tuno da cewa a lokacin da ta yi barazanar kashe kan ta ɗin, babu malamin da ya fito ya yi mata nasiha.
Ta ce: “In ban da zagi da na ke sha a gun jahilai babu wani babba ko babban malami daga malaman Nijeriya da ya kira ni ya min nasiha sai ita (kwamishinar).”
Mujallar Fim ta ruwaito tsohuwar jarumar ta na faɗin, “Da a ce na kashe kan nawa, to da manyan malaman Nijeriyan ba wanda ba zai hau mumbari ya tsine min ba saboda a ce su masu imani ne bayan kuma ni ban ga imanin ba. Don da akwai imanin, to da sun kira ni sun min nasiha a kan batun kashe kai na da na ce zan yi!
“Wallahi ko a Saudiyya ne, ina Musulma in furta kalmar zan kashe kai na, to da har limamin Harami sai ya kira ni ya min nasiha. Amma mu namu malaman ba ruwan su da rayuwar mu; rayuwar ‘ya’yan su ce kawai ta dame su, ba rayuwar ‘ya’yan wasu ba, bayan kuma Manzon Allah s.a.w. amana ya bar mu a gun su domin su zame mana gata, su dinga sa mu a hanyar shiriya da nasiha.”
A game da ziyarar da ta kai wa kwamishinar, Zee-Zee ta ce, “Na je mun zauna, ta min nasiha ne sosai mai ratsa jiki dangane da maganar ‘suicide’ da na ce zan kashe kai na.”
Ta ce ta faɗa wa kwamishinar matsalolin da su ka sa ta ce za ta kashe kan ta.
“Shi ne ta min alƙawarin share min hawaye na, ta kuma ci alwashin ba wanda zai sake take ni ya kwana lafiya a Nijeriya sai ta bi min haƙƙi na domin ita mace ce wanda ta ke kare haƙƙin rayuwar ɗan’adam, musamman mata, domin mata ta ke wakilta,” inji ta.
Zee-Zee ta ce bayan Malama Zahra’u ta gama yi mata nasiha, ta kuma kai ta gidan da gidauniyar ta ta ke inda ta ga yara marayu maza da mata da ta ke riƙo.
“Wallahi ban san lokacin da na fashe da kuka ba domin ni na daɗe ban ga mace mai imani da sanin darajar rayuwar ɗan’adam ba irin Malama Zahra’u,” inji ta.
Zee-Zee ta na cike da godiya ga kwamishinar saboda wannan “nasiha mai ratsa jiki” da ta yi mata.
Ta ce, “Ina godiya ta musamman zuwa ga kwamishinan, Malama Zahra’u, dangane da yadda ta nuna damuwar ta har ta buƙaci in zo ta ji matsalar da ta sa na ke son kashe kai na.”
Ta ƙara da cewa, “Sannan a da ban taɓa zaton a jam’iyyar APC akwai mutane masu imani irin na Malama Zara’u ba. To gaskiya daga yau zan fara girmama duk wani ɗan jam’iyyar APC saboda darajar karamci da ta min, ta kuma ce jahilci ne Musulumi ya ce zai kashe kan sa amma a hau zagin sa maimakon a yi maza a hana shi aikatawa, a kuma yi masa nasiha.
“Ina sake godiya Dakta Malama Zara’u. Allah Ubangiji ya yafe miki zunuban ki tun ki na raye, ya kuma biya miki buƙatun ki na duniya da lahira, sannan ya ba ki Aljanna Fiddausi, amin.”