Ali Nuhu ya bayyana cewa bai goyi bayan Rahama Sadau ko wani jarumi daga masana’antar shirya finafinan Hausa ba, wato Kannywood. Ya ce korar dan fim ya na da hatsari babba.
Jarumin Jaruman, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Kannywood, ya bayyana haka ne a wata doguwar tattaunawa da ya yi da mujallar Fim kwanan nan.
Haka kuma ya yi magana kan ’yan rigingimun industiri da su ka faru a cikin 2016 inda sunan sa ya fito, misali sabanin da ya faru tsakanin Adam A. Zango da Rahama Sadau wanda ya shafo Alin, da maganar sabon fim din sa mai suna ‘Mansoor’ wanda ya gama shiryawa kwanan nan, da batun wasu ke yi na cewa tunda an kori Rahama, to shi Alin me ya sa ba za a kore shi ba? Da sauran su.
An dade ba a ji daga bakin jarumin ba a mujallar Fim, sai dai ’yan labaran da su ka shafe shi. Ga shi kuwa ya yi abubuwa masu damar gaske a cikin ’yan shekarun nan. Ya yi tafiye-tafiye, ya fito a finafinai ba iyaka, ya karbi kyaututtukan karramawa.
Bayan haka, akwai kallon da wasu ke yi masa, har su na fadin bakaken maganganu a kan sa. Shin menene ra’ayin sa kan wadannan abubuwan? Shin shi kan sa me ya ke ciki? Wadanne nasarori ya samu cikin ’yan watannin nan? Me ya sa a gaba? Me zai ce kan ’ya’yan sa da ke yin fim? Yaya dangantaka ta ke tsakanin sa da Adam A. Zango da kuma Zainab Indomie? Me zai ce kan satar fasaha da ake yi wa ’yan fim?
Mujallar Fim ta zanta da Ali Nuhu game da wadannan al’amura da mu ka lissafa maku a sama. Hira ce irin wadda Ali ya dade bai yi irin ta ba, domin fa babu kama hannun yaro. Mun yi masa tambayoyin da, da alama, ya ji dadin su, to amma akwai wadanda kai daga jin amsar sa ka san bai ji dadin su ba. To, aikin jaridar kenan!
Ku nemi mujallar Fim ta wannan watan a kasuwa, ku sha hirar mu da Sarki Ali Nuhu.