MAWAƘI Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) ya bayyana cewa bai san ya Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta kai shi ƙara ba kamar yadda aka yaɗa a kafafen yaɗa labarai.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin cewa hukumar ta maka shi a kotu sakamakon fitar da wata da ya yi ba tare da an tace ta a hukumar ba.
Mutane sun zuba ido domin jin yadda za ta kasance, musamman ma dai ganin cewa mawaƙin bai halarci zaman kotun ba, kuma bai tura lauyan sa ba.
Mai magana da yawun sa, Abdullahi Alhikma, ya bayyana cewa babu wata hukuma da ta kai Rarara ƙara, su ma kawai a soshiyal midiya suka ji amma takardar Sammacin ba ta zo gare su ba.
Alhikma ya ce: “Wannan takarda da muka ga tana yawo a kafafen sadarwa wacce wata hukuma a Jihar Kano ta maka mawaƙi Dauda Kahutu Rarara a kotu, to wannan sanarwa mu ma mun gan ta ne a kafar sadarwa na cewa an kai kotu.
“Kuma mun san in ana ƙarar mutum to za a je ne inda za a kai takarda ta sammaci a gidan sa ko wani waje da za a same shi.
“To mu dai ba mu ga wannan saƙo ba, sai a kafar sadarwa ta midiya. A saboda haka wannan takarda mu ba ta same mu ba.

“Kuma a sanarwa da aka bayar a soshiyal midiya ma mu ba mu ga an ce ga kotun da ake neman mu ba ko kuma ga ma waƙar da aka yi.
“Na ji wani da yake magana da yawun Hukumar Tace Finafinai waƙar ma ya kasa faɗar sunan wacce waƙa ce. Kuma mun yi waƙoƙi da yawa a wannan wata waɗanda aka sake su.
“Ya kamata ya fito ya bayyana wacce waƙa ce, tunda dai abin a midiya muka ji sai mu ji mu ma kuma ba mu san kotun da aka kai ƙara ba. Don haka ya kamata dai mu sani.
“Don shi abu idan aka ce kotu babu wanda ya fi ƙarfin kotu. Ko Shugaban Ƙasa ne aka ce an kai shi kotu, to dole zai san wacce kotu aka kai shi, kuma a kan wanne laifi ake neman sa.
“To kuma mu ma ‘yan ƙasa ne masu biyayya ga dokokin ƙasa. Saboda haka mu ba ma raina kotu, kuma ba ma raina hukuma, amma dai wannan takarda ta wannan sammaci da ake faɗa a kafar sadarwa muka ji shi, kuma ita kotu ko hukuma ta san inda ake neman mutum in ana neman sa.
“Muna zaton dai ko ɗan aiken ne bai ƙaraso gare mu ba har zuwa yanzu.
“Kuma a yanzu shi Dauda Kahutu Rarara ba wai yana yin waƙoƙin sa a nan Jihar Kano ba ne, ko kuma yana yin waƙoƙin sa a kan iya Jihar Kano.
“Asali ma waƙoƙin a Abuja ake yin su. Duk lokacin da ka ga ya zo Kano, to wani uziri ne ya kawo shi, kuma zai yi ya gama kwana ɗaya biyu ya fita.
“Don haka yanzu ya bar Kano ya koma Abuja. To saboda haka ba mu san a ina aka kai wannan takarda ba, kuma har yanzu ba ta riske mu ba. In da ta riske mu to za mu yi wa doka biyayya. Sai mu sa lauyoyin mu su je su ji ba’asi na abin da ake tuhumar mu da shi, tunda dukkan mu a ƙarƙashin doka muke kuma babu wanda ya fi ƙarfin doka.”
A nata ɓangaren, hukumar ta yi martani kan iƙirarin Rarara.
A martani, kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya faɗa a sanarwar da ya fitar cewa: “Tun a ranar 8/11/2024 kotun mai lamba 47 da ke unguwar Noman’sland a Jihar Kano ta aika wa da mawaƙin takardar sammaci a ofishin sa da ke kan titin gidan Zoo a Kano kuma bayan rashin samun sa kotun ta ƙara tura masa da saƙon kar-ta-kwana ta hanyar text message tare da manhajar WhatsApp inda aka buƙaci ya bayyana a gaban kotun a ranar 13/11/2024.
“Dangane da maganar da wakilin mawaƙin ya yi na cewa ba a Kano mawaƙin ya yi waƙar ba, hakan ya tabbatar da cewa mawaƙin ya kwana da sanin laifin da hukumar take zargin ya aikata.
“Haka kuma yana da kyau al’umma su ƙara fahimtar cewa matsawar ɗan fim, marubuci ko mawaƙi ya taɓa yin rijista da hukumar to dole ne ya bi dokokin hukumar a duk inda yake kamar yadda ya ɗauki alƙawari a yayin da zai cike fom.
“Bugu da ƙari, hukumar na da hurumi na saka ido, ba da shawara ko hukunta duk wani aiki da ya shafi ayyukan da suka rataya a kan ta matsawar ya shigo Jihar Kano ko a ina aka yi aikin.”
![]()







