• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ban taɓa ganin irin wannan karramawar da aka yi min ba, inji Rikadawa

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 15, 2023
in Labarai
0
Rikadawa riƙe da kambin karramawar sa

Rikadawa riƙe da kambin karramawar sa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMIN Kannywood, Rabi’u Muhammad Rikadawa (Baba Ɗan Audu), ya bayyana farin cikin sa game da karramawar da ya samu daga ‘Our Nigerian News Magazine’, wanda shi kaɗai ne ya samu wannan karrama a masana’antar finafinan Hausa.

Mujallar Fim ya zanta da shi a kan wannan karramawa da ya samu na gwarzon jarumi (Best Actor), inda ya fara da cewa, “Wato a dukkanin karramawa da na ga ana yi a tsawon rayuwa ta a wannan masana’anta, zan iya cewa ni ban taɓa ganin karramawa irin wannan ba. Saboda karramawa ne wanda su su ke yi, ni ban san su ba, ko labarin su ban taɓa ji ba a duniya, su su ka bincika, su ka ji wanene ni, da me da me da me na yi? Da su ka fara ba ni labarin wasu abubuwa dangane da ni kai na, a gaskiya mamaki na yi. So, kusan dukkanin waɗanda su ka karrama a irin haka su ke zuwa.”

Dangane da yadda ya ji game da karramawar, Rikadawa ya ce, “Na yi farin ciki matuƙa, saboda in ka lura yadda su mashirya taron su ke, ‘Our Nigerian Magazine’ ne. In ka kula a irin tsarin su, kamar yadda sunan ya ke, kusan daga kowane ɓangare na rayuwa, Nijeriyan kaɗai su ke kallo. Za ka ga da su Buratai, sarakuna da sauran manyan mutane, za ka ga kowanne daga kowane sassa na Nijeriya aka ɗauko kamar yadda sunan abin ya ke. Duk irin abin da ka ke yi ko yaya ya ke, su irin abin da su ke yi kenan, su kan duba ta ina ka ke bada gudunmawa, ka ke taimakawa ƙasa, sai a karrama mutum ta irin wannan. Wannan shi ne abin burgewa da ya ba ni sha’awa. Yadda su ka ce sun duba ni, domin binciken jama’a ne, jama’a su ka zaɓa, su ka ce abin ya yi, sannan su ka ba ni.”

Janar Yusuf Tukur Buratai na miƙa wa Rikadawa kambin karramawar sa

Jarumin ya ce ya yi matuƙar murna da farin ciki a kan wannan karramawa. Kuma na yi wa Allah godiya.

Rikadawa ya samu karramawar a matsayin na biyu kenan a wannan shekara. 

A kwanakin baya an karrama shi a ‘Arewa Heroes & Philanthropic Award of Excellence’ tare da wasu jarumai da wasu manyan ƙasar nan. 

Wannan taron na ‘Our Nigerian News Magazine’ an gudanar da shi ne a ranar Asabar, 11 ga Nuwamba, 2023 a ɗakin taro na International Conference Center, Abuja.

Wani sashe na mahalarta taron
Rikadawa na jawabin godiya
Kambin karramawar Rabi’u Rikadawa

Loading

Previous Post

Mutuwar Samanja babbar asara ce ga ƙasa, inji Tinubu

Next Post

Ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun haɗa kai wajen yin tir da hare-haren Isra’ila a Zirin Gaza

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Shugaba Tinubu a wajen taron na OIC

Ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun haɗa kai wajen yin tir da hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!