• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Bikin baje-kolin finafinai na Zuma 2024: Ali Nuhu ya gana da ƙaramar ministar Abuja

by ABBA MUHAMMAD
July 13, 2024
in Labarai
0
Bikin baje-kolin finafinai na Zuma 2024: Ali Nuhu ya gana da ƙaramar ministar Abuja

Ali Nuhu da Minista Mariya tare da sauran jami'an gwamnati

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MANAJAN Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), ya gana da , Ƙaramar Ministar Gundumar Babban Birnin Tarayya, Abuja, Hajiya Mariya Mahmud Bunkure, a ofishin ta da ke Abuja, inda su ka tattauna haɗin gwiwa yayin gabatowar bikin baje-kolin finafinai na Zuma a daidai lokacin da aka fara shirye-shiryen gudanar da na wannan shekarar ta 2024.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa akan yi bikin ne a duk shekara.

Haɗin gwiwar NFC da gwamnatin gundumar Abuja ya ta’allaƙa ne kan binciken sababbin dabaru don ɗaukaka bikin zuwa sabon matsayi.

Ali Nuhu ya duƙufa wajen inganta masana’antar finafinan Nijeriya da bunƙasa al’adun ƙirƙire-ƙirƙire da ƙwarewar sa.

A yayin gudanar da taron, shugaban na NFC ya ce, “Mu na da burin mayar da bikin finafinai na Zuma na 2024 ya zama wani muhimmin al’amari, wanda zai nuna mafi kyawun basirar mu a finafinai.

“Haɗin gwiwar NFC da ministan FCT ya na da muhimmanci mai ƙarfi wajen cimma burin mu tare da sha’awa da azama.

“Mu na shirye don gudanar bikin da ba za a manta da shi ba, wanda zai bar tarihi mai ɗorewa ga masu kallo da masu shirya finafinai.”

Jami’an NFC da na FCTA su na tattaunawa

A nata ɓangaren, ministar ta ce ba ta da wata shakka wajen samun nasara a wannan ƙudiri na haɗin gwiwa na abokan hulɗar biyu.

Ta ba da tabbacin cewa FCT za ta taka rawar gani wajen tabbatar da an cimma manufofin bikin baje-kolin finafinan.

Hajiya Mariya Mahmud Bunkure ta na jawabi
Hoton ɓangarorin biyu bayan taron

Loading

Tags: Ali Nuhubikin baje-kolin finafinaiMariya Mahmud BunkureZuma Film Festival
Previous Post

Kwaɓa a ‘Labarina’: Ma’aikatan jinya na so darakta Aminu Saira ya ba su haƙuri

Next Post

Ɗan Kannywood, Ibrahim Wassh ya samu Zahra

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Ɗan Kannywood, Ibrahim Wassh ya samu Zahra

Ɗan Kannywood, Ibrahim Wassh ya samu Zahra

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!