Fitacciyar jarumar Kannywood, Asma’u Abdullahi Wakili, wadda aka fi sani da Asmee Wakili, ta yi bikin zagayowar ranar haihuwar ta tare da yin wani abin alheri da kowa yake yaba mata.
A ranar Juma’a, 29 ga Agusta, ne jarumar ta shirya bikin inda ta ziyarci gidan ajiya da gyaran hali na Gwauron Dutse, Kano, kuma ta biya tarar wasu da suke tsare a gidan domin su shaƙi iskar ’yanci.
Asma’u tare da fursunonin da ta ‘yantar
Jarumar ta bayyana wannan abin da ta yi a wani ɓangare na shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar ta, inda ta ce tana ganin hakan ya fi dacewa saboda nuna tausayin ta ga masu ƙaramin ƙarfi da Allah ya jarabce su da shiga wannan hali na zama a gidan gyaran hali sakamakon wata ƙaddara da ta same su.
Ta ce: “A matsayi na na mace mai tausayin rayuwar raunana, na daɗe ina da wannan tunanin da kuma fatar Allah ya ba ni damar yin hakan.
“Don haka nake yi musu murna da samun ’yanci, da fatar Allah ya kiyaye gaba. Kuma Allah ya tsare al’umma daga shiga irin wannan hali na jarabawa.”
Jama’a da dama a soshiyal midiya sun yi wa Asma’u fatar alheri da sanya mata albarka, bayan nuna godiyar ta ga Allah da ya raya ta har ta yi murnar ƙarin shekara, amma ta tuna da waɗanda suke tsare a gidan yari.