A YANZU ana samun ƙarin shigowar mata cikin harkar bege, wato yabon Manzon Allah (s.a.w.). Ana iya cewa matan ma sun fi mazan yawa a cikin harkar.
Maimuna Ibrahim Isma’il (Ummi Burdatu) ta na ɗaya daga cikin sha’irai mata da su ke tashe a yanzu. Ta yi waƙoƙi da dama na yabon Manzon Allah (s.a.w.).
Mujallar Fim ta tattauna da ita dangane da tarihin ta da yadda ta shiga sha’anin bege da kuma hangen da ke yi wa harkar, kamar haka:
FIM: Da farko, ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
UMMI BURDATU: To, da farko ni dai suna na Maimuna Ibrahim Isma’il, amma dai an fi sani na da sunan Ummi Burdatu. An haife ni a Darki ta Ƙaramar Hukumar Wudil da ke Jihar Kano a shekarar 1998. Sai dai mun dawo garin Kano a 2004.
Na yi Makarantar Firamare ta Kabiru Ƙiru da ke unguwar Sharaɗa. NZa yi Ƙaramar Sakandare Salanta Sharaɗa. Na yi babbar sakandare ta GGSS Ja’en Sabon Gida. A yanzu kuma ina Aminu Kano College, ina shekara ta ƙarshe.
A ɓangaren karatun Arabiyya, na yi Islamiyyu aƙalla guda uku inda na yi saukar Alƙur’ani tare da hadda, kuma na sauke wasu littattafai.
FIM: Yaya aka yi ki ka samu kan ki a cikin harkar yabon Manzon Allah (s.a. w.)?
UMMI BURDATU: Gaskiya na samu kai na a harkar yabon Manzon Allah (s.a.w.) tun ba ni da wayo saboda na kasance ma’abociyar son waƙa tun ina yarinya. Har a kan ba ni labarin cewa ko aike na aka yi ina dawowa, da waƙa ake gane na dawo; ita ce sallama ta.

To, inda na fara ƙasida a wata makaranta ce da na taɓa yi, Hidayatus Sufya, inda na fara da yin amshi. To da Mauludi ya zo sai aka ba ni na yi. Haka dai ana ta tafiya na fara rubuta baiti biyar zuwa sama har na zo Ɗariƙun Huda na yi ƙasida mai baiti 15. A nan malamai su ka zauna su ka duba, aka kira ni aka tambaye ni ko za a bar ni a gida na je situdiyo? Na ce ban sani ba, amma ina tsoro saboda gidan mu ‘yan Izala ne. Kafin wannan ma akwai makarantar da na yi wadda a nan ma ina yin waƙar da baki, sai malamin mu ya nemi mu je da sauran ɗalibai ya yi ƙasida za mu hau, aka hana ni a gida. To a wannan makaranta Ɗariƙul Huda nan ne na yi nasara na fara shiga situdiyo a shekarar 2017. Wannan shi ne tarihin fara yabon Manzon Allah (s.a.w.) a waje na.
FIM: Ita harkar yabon a yanzu wasu su na rubutawa da kan su su rera, wasu kuma ana rubuta masu a rera sai su hau karin. Ke a wane matsayi ki ke?
UMMI BURDATU: E, gaskiya akwai ƙasidu na, ni na rubuta na rera, kamar guda biyar. Akwai waɗanda rubuta mani aka yi, kamar biyar su ma, sannan rubutattun da na ke da su cikakku wanda na gama aiki kawai su ke jira Allah ya hore aƙalla sun kai guda takwas; sai waɗanda ba a kai ga kammala su ba, su ma su na da yawa.
FIM: To wace ƙasida ce ki ka yi ta farko da ta fito da ke?
UMMI BURDATU: Ƙasida ta ta farko ita ce ‘Labbaika Annabin Allah, Barka Da Zuwa Ma’aiki Na, ‘Yan Ɗariƙul Huda Mu Na Son Ka Karɓi Roƙo Na’. Na yi wannan ƙasidar ne a 2017. Don haka zuwa yanzu ina da ƙasidu bugaggu sun kai guda goma. Amma dai ban yi album ba, sai nan gaba.
FIM: Me ya fi burge ki a cikin harkar yabon Manzon Allah (s.a.w.)?
UMMI BURDATU: Abin da ya fi burge ni shi ne yadda mu’amala ta ta ke kasancewa da mutane; ka kusanci kowa ba kyara ba ƙyama; sha’irai manya da ƙanana a haɗu cikin shauƙin hirar Ma’aiki; da yadda ake taron wayar da kan sha’irai, abin ya na burge ni.
FIM: Ko akwai wasu matsaloli a cikin harkar yabo da ku ke yi?
UMMI BURDATU: Gaskiya akwai matsaloli jingim. ‘Ya mace in ta na harkar yabon Manzon Allah (s.a.w.) abin da ya shafi zuwa situdiyo, har yau kai bai gama wayewa da zuwa situdiyon ‘ya mace ta je sai a riƙa yi mata wani irin kallo na daban. Sannan yawan fitar sha’irai mata majalisi ko wani taro, ka fita yau ka fita gobe, ko a sati ka fita sau uku, shi ma ‘yan unguwar ku su na yi maka wani irin kallo mai kama da “ina ta ke zuwa?”
Sannan har yanzu ba a fiye yarda ‘ya’ya mata su na da zurfin ilimin da za su faɗi wata kalmar ga Shugaba ba, sai a ga in dai ba rubutawa aka yi aka ba su ba, to ba za su iya ba; to ba haka ba ne.
FIM: Ana ganin ku mata masu yabon Annabi auren ku ya na da wahala.
UMMI BURDATU: A’a, babu wani wahala. Ai mata masu yabo ba su da wani buri da ya wuce haɓaka sunnar Shugaba (s.a.w.). Farin cikin sa fa mu ke nema. Gaskiya wannan tunanin bai yi daidai ba; duk wanda ya ke yi, to ya daina. Mata nawa ne su ka fara suna, ‘yanmata kuma, su ka ci gaba da yi bayan sun yi aure? Kuma ko ba su ci gaba ba su na zama su raya sunna. Tunda da ma ma ai sunnar su ke so su ɗabi’antu da shi, me ya rage? Ai mu burin mu bai wuce yardar Allah da samun matsayi cikin fadar Shugaba ba.
FIM: A yanzu wane buri ki ke da shi a fagen yabon Manzon Allah?
UMMI BURDATU: Buri na na ga an saita hanya a yabo, an gyara kurakurai, musamman na furucin kalma. Domin akwai furucin da bai kamata a yi wa Manzo da sigar furucin ba, akwai kalmomin da ba su cancanta ba a saka su a sahun ba, kamar kalma mai harshen damo ba a saka ta a bege, ta na ba da ma’ana biyu; kai mai yabo har zuciyar ka mai kyau ka ɗauka, shi mai sauraro sai ya ɗauke ta a marar kyau. Ka ga wannan ta na haɗa jayayya. Allah ya shiga lamarin mu.
FIM: A ƙarshe, wane kira ki ke da shi ko shawara?
UMMI BURDATU: A ƙarshe, ina so na yi amfani da wannan damar na ƙara gode wa Allah tare yi wa ƙungiyoyi na addu’a, Budatul Madihi fi Madahin Nabiy Sallallahu Alaihi Wa Sallam wacce ta ke rajin kare janibin Shugaba (s.a.w.) tare da tsaftace kalamai a yabon Annabi wanda ko yaushe shi ne aikin ta, shi ta sa a gaba. Allah ya ci gaba da yi wa shugabanni jagora. Sai kuma Sha’iran Annabi ta Jihar Kano Group WhatsApp wacce ta ke fafutikar haɗa kan sha’irai tare da wayar da kai a cikin yabo don ganin an gudu tare an tsira tare. Allah ya ci gaba da yi masu jagoranci, amin.