• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Burin Platinum Cinema shi ne ta haɓaka Kannywood – Babatunde Adeniji

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
July 30, 2021
in Tattaunawa
0
Burin Platinum Cinema shi ne ta haɓaka Kannywood – Babatunde Adeniji
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN daɗe babu isassun gidajen sinima inda za a riƙa nuna finafinan Hausa a Kano. Hakan ya faru tun lokacin da aka ƙaddamar da mulkin Shari’a a jihar a shekarun baya, wanda ya janyo rufe sinimu da gidajen kallo.

Tsawon lokaci, gidan sinima na Filmhouse da ke rukunin kantuna na Shoprite kaɗai ne ke nuna finafinan. Wannan ya sa masu shirya finafinai su na kukan matsalolin da hakan ya haifar, musamman kuma da yake kasuwar fayafayen fim ta durƙushe.

Ana cikin wannan yanayi, kwatsam, sai aka samu ɓullar wani sabon gidan sinima a Kano wanda ya zo da zummar ciyar da masana’antar Kannywood gaba da samar da kuɗin shiga ga masu shirya finafinan Hausa. Sinimar, mai suna Platinum Cinema, ta na Titin Zariya ne.

Shin da wacce ta zo? Mujallar Fim ta tattauna da shugaban sinimar, wato Babatunde Adeniji, domin jin dalilin su na kafa buɗe wannan wuri da irin haɗin gwiwar da za su yi da ‘yan fim domin fidda jaki daga duma.

FIM: Ko za ka iya faɗa mana kaɗan daga cikin abin da wannan sinima ta zo da shi?

BABATUNDE ADENIJI: Platinum Cinema sinima ce da wasu gungun mutane su ka haɗu domin samar da ita tare da kyakkyawan ƙudiri da manufa domin bai wa mutanen Kano wani abu na daban wanda ba su saba ga ni ba. An ɗauki tsawon shekaru Kano na da sinima ɗaya tilo, wanda hakan ya tauye wa masu shirya finafinai damarmakin kawo finafinan su a haska; saboda ɗaya ce, dole sai wani ya gama da nasa kafin a fara haska naka.

Ganin haka ya sa mu ka yi tanadin yanayi mai kyau domin waɗanda za su zo kallon finafinan Hausa da sauran su su samu natsuwa da jin daɗi da kuma samar da yanayin kasuwanci mai kyau tsakanin mu da abokan hulɗar mu.

FIM: Ya tsarin wannan sinima ya ke ta fuskar girma?

BABATUNDE ADENIJI: A gaskiya Mun tsara sinimar mu ta hanyar yin ɗakunan kallo wanda mutane za su zauna cikin sakewa ba tare da wani ya takura wa wani ba, sannan mun tanadi isassun jami’an tsaro tsawon awa 24.

FIM: Da yake Kano ce cibiyar shirya finafinan Hausa, zuwa yanzu akwai wata yarjejeniya ta haɗaka tsakanin ku da ‘yan masana’antar ta fuskar ba ku fim?

BABATUNDE ADENIJI: Mun yi sosai ma, domin kuwa dukkan masu shirya finafinai da jarumai mun ƙulla alaƙa da su, kamar irin su Maishadda, Ali Jita, Sheikh Isa Alolo, Adam A. Zango, da dai sauran su. Mun fahimci juna da su sosai.

FIM: Tun bayan buɗe wannan sinima, kimanin finafinan Kannywood nawa aka haska zuwa yanzu?

BABATUNDE ADENIJI: To zuwa yanzu dai a fim na biyu mu ke. Mun haska fim mai suna ‘Shaheeda’ da kuma wanda mu ke haskawa yanzu, sai kuma wanda za mu fara haskawa a wata mai zuwa.


FIM: Akwai wasu sharuɗɗa ko matakai da ake bi idan furodusa ko darakta ya na so a haska fim ɗin sa?

BABATUNDE ADENIJI: E, akwai mana, wato kyawun aikin ka ta fuskar kyakkyawan labari da kayan aiki wanda idan mutane sun gani za su yarda da cewa wannan fim ne.

Gidan sinima na Platinum, Kano

Don haka duk wanda ya san ya na da fim wanda ya san cewa ya yarda da kyan aikin da ya yi masa, to ya zo ya kawo, mu na maraba da shi.

FIM: Ya maganar samun haɗin kai tsakanin ku da ‘yan fim?

BABATUNDE ADENIJI: Mu na samu domin wanda mu ka ɗauko ya zama wakilin mu, wato ambasada, daga cikin wannan masana’anta ya ke, wato jarumi Yakubu Muhammad, kuma sananne ne shi. Gaskiya mu na samun kulawa kuma da man tun kafin a buɗe wannan sinima mu na da kyakkyawar alaƙa tsakanin mu da su.

FIM: Iya fim ɗin Hausa ake nunawa a wannan sinima?

BABATUNDE ADENIJI: Mu ba mu tsaya iya haska fim ɗin Hausa ba kawai, mu na haska su Bollywood da su Nollywood. Kuma sinima ce mai rijista domin ta na da damar haska duk wani fim da ta ga dama in dai bai saɓa wa doka ba.

FIM: Wane buri ku ke so ku cimmawa?

BABATUNDE ADENIJI: Burin mu shi ne mu na so mu mamaye dukkan faɗin Jihar Kano. Mu na da burin kafin ƙarshen wannan shekarar mu ƙara buɗe wata sinimar a Kano domin faranta wa mutanen Kano rai.

FIM: Menene saƙon Platinum ga jama’a?

BABATUNDE ADENIJI: Jama’a ya kamata su san cewa wannan fa sinimar tasu ce, kowa ya na da damar da zai iya zuwa domin kuwa mun tanadi isassun jami’an tsaro tare da wurin wasanni na zamani, sannan mu na da duk wani abu da masoya sinima su ke da buƙata wanda zai ɗauke musu kewa. 

Kuma mu na maraba da kowa da kowa. Ku zo mu cicciɓa harkokin finafinai tare domin ci gaba da samar wa matasa da ayyukan yi da rage zaman banza tsakanin su.

Harabar karɓar baƙi ta Platinum Cinema
Mista Tunde Adeniji

Loading

Tags: Babatunde Adenijicinemas in KanoFilmhousehausa filmsKannywoodPlatinum Cinema
Previous Post

Doka ce ta cire Sunusi Oscar442 daga fim ɗi na ba Afakallah ba – Alhaji Sheshe

Next Post

Tasirin kallon finafinan Hausa ne ya sa na musulunta – Rahma A. Ibrahim

Related Posts

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje
Tattaunawa

Abin da ya sa zan shirya fim mai dogon zango – Kabiru Jammaje

December 14, 2025
Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali
Tattaunawa

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

October 13, 2025
Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV
Tattaunawa

Tarbiyya a Kannywood: Bai kamata laifin wasu ya rinƙa shafar wasu ba – Maryam CTV

September 29, 2025
Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa
Tattaunawa

Rashin tsayayyen ubangida ke hana wasu jarumai yin suna – Mama Siddiqa

September 14, 2025
Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu
Tattaunawa

Bayan damfarar kuɗin magani: Halin da jaruma Halisa Muhammad take ciki yanzu

September 1, 2025
MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano
Tattaunawa

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

June 30, 2025
Next Post
Tasirin kallon finafinan Hausa ne ya sa na musulunta – Rahma A. Ibrahim

Tasirin kallon finafinan Hausa ne ya sa na musulunta – Rahma A. Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!