FITACCIYAR jarumar Kannywood Hadiza Gabon ta bayyana cewa shari’ar da ake tafkawa da ita a Kaduna ta jefa rayuwar ta cikin haɗari.
Ta faɗi haka ne a gaban alƙalin kotun Shari’ar Musulunci da ke Magajin Gari, Kaduna, a yau Litinin a cigaba da sauraren ƙarar ta da wani mutum ya kai ta.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa ya maka ta a kotun bisa zargin cewa ta ci masa kuɗi har N396,000 sannan ta ƙi auren sa.
Jarumar, wadda ke zama a Kaduna, ta faɗa wa kotun a zaman da aka yi a baya cewa wannan magana dai zuƙi ta malle ce, domin ita ba ta ma san mutumin ba.
Alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar daga ranar 28 ga Yuni, 2022, zuwa yau, 1 ga Agusta, saboda rashin lafiyar matar sa.
A yau ne aka ba Musa damar ya kawo shaidun da ya ce ya na da su.
Sai dai Hadiza Gabon ta shaida wa kotun, ta bakin lauyan ta, Barista Mubarak Sani Jibril, cewa taɓarɓarewar tsaro a ƙasar nan ya sa jarumar ta na jin tsoron zuwa kotun.
Ya ce jarumar ta na tsoron yadda a duk ranar da aka dawo kotu domin cigaba da sauraron ƙarar sai an yi dabarar ficewa da ita daga kotun.
Lauyan ya ce: “Tsaron lafiya ta ya na da muhimmanci, ita ma tsaron lafiyar ta ya na da muhimmanci, sannan tsaron lafiyar sauran jama’a ma ya na da muhimmanci a kotun, har ma da shi mai ƙarar.
“Rayuwa ta ta na cikin haɗari, rayuwar ta ta na cikin haɗari, rayuwar shi ma mai ƙarar ta na cikin haɗari. Ba mu san waye ke bibiyar shari’ar a soshiyal midiya ba. Abu na gaba shi ne za ka fara ganin ‘yan bindiga a nan sun zo satar mutane domin garkuwa da su. Wannan shi ne abin da ya dame mu, ba shari’ar da ake yi a kotu ba.”
Lauyan ya yi kira ga alƙalin da ya yi la’akari da tsaron lafiyar wadda ake ƙara ya ba ta damar ta daina zuwa kotun domin cigaba da sauraron ƙarar.
Da jin haka, sai lauyan mai ƙara, wato Barista Naira Murtala, ya ƙi amincewa da wannan roƙon, ya ce tilas ne wadda ake ƙarar ta zo kotu a ko yaushe.
A kan batun tsaron lafiyar wadda ake ƙarar kuwa, ya ce ba zai ƙi amincewa da roƙon da su ka yi ba saboda da gaske ne babu tsaro ga kowa a ƙasar, to amma akwai buƙatar su kawo shi a rubuce domin ya duba ya yi nazari.
Alƙalin kotun, Khadi Rilwanu Kyaudai, ya ba su tabbacin cewa kotun za ta duba batun tsaron lafiyar masu shari’ar a zaman kotun na gaba.