• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mun sauya ofis ne saboda kiyaye mutuncin Kannywood – Alhasan Kwalle

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
August 1, 2022
in Labarai
0
Malam Alhassan Kwalle

Malam Alhassan Kwalle

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TUN  bayan buɗe sabon ofis da Ƙungiyar Jaruman Kannywood ta Jihar Kano ta yi daga bayan Kantin Jifatu da ke Titin Zariya zuwa Titin Adamu Ɗankura  da kuma zaman da sauran shugabannin ta irin su Tijjani Asase da Ƙazaza su ke yi a tsohon ofin ɗin ake ta yaɗa maganganu a kan ƙungiyar, har ana cewa ta rabu gida biyu.

Da mujallar Fim ta nemi jin ta bakin shugaban ƙungiyar, Malam Alhasan Kwalle, sai ya shaida mana cewa,”Ƙungiyar Jarumai ba rabuwa ta yi ba, mu na nan a tare mu na aiki tare, kawai dai an samu sauyin ofishin ƙungiyar ne daga bayan Jifatu zuwa Titin Adamu Ɗankura.”

A kan dalilin ci gaba da ganin tsohon ofishin a buɗe kuma sauran shugabannin ƙungiyar su na a zaune a wajen su na gudanar da harkokin su, Alhassan, wanda ake wa laƙabi da Baƙin Wake, ya ce, “Wannan haka ne. Su Tijjani Asase su na tsohon ofin. Amma ba da sunan Ƙungiyar Jarumai su ke zama ba. Su na zama ne a matsayin kamfanin su da su ke gudanar da harkar fim ɗin ‘A Duniya’. Don haka duk wani abu da ya shafi aikin fim ɗin a ciki su ke yi, amma ba na Ƙungiyar Jarumai ba ne.”

Da mu ka tambaye shi dalilin tashin ofis daga wajen tunda ba rabuwa aka yi ba, sai ya ce, “To gaskiya wajen tun farko da mu ka zauna mu kaɗai ne a wajen, a yanzu sai ya zama an buɗe wajen shaƙatawa a wajen, sai ya zama samari da mata su na zuwa, kuma akwai waɗanda ba abin kirki ya ke kawo su wajen ba. 

“Kuma ‘yan Hisbah su na yawan kawo hari wajen. To kuma daga sun zo, sai matan su riƙa zuwa su na shiga ofishin mu su na ɓuya, don haka sai ya zama ana tunanin ‘yan fim ne. Don akwai lokacin da har ciki ‘yan Hisbah su ka shiga su ka kamo wasu matan.

“To wannan ya sa mu ka ga ana nema a ɓata wa harkar fim suna. Don haka sai mu ka tashi daga wajen, domin zaman mu a wajen zai iya kowa ɓata sunan masana’antar fim, mu kuma ba don haka mu ke zama a wajen ba.

“Kuma tun da abin ya zo da haka mu ka ga ya dace mu bar wajen, mu koma wajen da za mu kiyaye martabar masana’antar, domin ba za mu so harkar da mu ka ɗauki shekaru mu na ƙoƙarin gyara ta ba kuma wani abu ya zo wanda zai mayar da hannun agogo baya ba, don haka ne mu ka tashi daga wajen.”

Alhasan Kwalle ya yi kira ga ‘yan fim da su riƙa kiyaye mutuncin su da na sana’ar su a duk inda su ka samu kan su.

Loading

Tags: A DuniyaAlhassan KwalleartistesHisbahjarumaiKannywoodKanoƘazazaƙungiyaofisTijjani Asase
Previous Post

Cewar Hadiza Gabon a kotu: Rayuwa ta ta na cikin haɗari

Next Post

Mun dawo da Gidauniyar Kannywood saboda wasu dalilai – Alkanawy

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Malam Ahmad Salihu Alkanawy

Mun dawo da Gidauniyar Kannywood saboda wasu dalilai - Alkanawy

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!