FITACCIYAR jarumar masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, Hajiya Ladidi Fagge, ta bayyana cewa labarin da ake bazawa cewa ta rasu ba gaskiya ba ne.
An jima ana baza labari a soshiyal midiya cewa jarumar ba ta da lafiya, ta na kwance cikin wani mawuyacin hali, har ana haɗawa da wani hoto inda ta rame matuƙa.
Akwai ma masu cewa wai ta rasu.
Ganin yadda labarin ya yaɗu kamar wutar daji ya sa mujallar Fim a jiya Alhamis ta nemi jin ta bakin ta, inda ta ce ita ba ta ma san ana yaɗa wannan labarin ba saboda ba ta samu zama ba da har za ta hau intanet ta ga abin da ake rubutawa.
Dangane da ko ta yi rashin lafiya kuwa, Hajiya Ladidi ta faɗa wa wakilin mu a Kano cewa: “Tabbas, a baya na yi rashin lafiya, amma ba yanzu ba ne, tun a watannin baya ne. Kuma na samu sauƙi na ci gaba da harkoki na, don a yanzu ma da na ke magana da kai anjima kaɗan zan tafi aikin fim ɗin ‘Alaqa’ a unguwar Maidile.”
Ta ci gaba da cewa, “Ko a kwanakin baya gidan Rediyon Arewa sun kira su ka ce wai sun samu labarin ba ni da lafiya ina neman taimako na kuɗi da na addu’a. Sai na ce ni dai ban faɗa wa kowa ina neman taimako ba, amma dai idan wani ne ya ga dacewar hakan ya ce zai ba ni wani abu na taimako to hakan ba zai zama abin da zan ce ba na so ba; kuma maganar ina buƙatar a taya ni da addu’a, to ai ba sai mutum ya na kwance zai buƙaci addu’a ba. Ina buƙatar addu’a a wajen masoya na a yanzu da kuma kowane lokaci.”
Jarumar ta yi fatan alheri ga dukkan masoyan ta saboda damuwar da su ka nuna a game da labarin da su ka gani ana yaɗawa.
Comments 1