LAWAL Ibrahim Gungun, wanda aka sani da Bawan Mata, ya na ɗaya daga cikin jarumai maza da tauraron su ke haskawa a cikin finafinan barkwanci na wannan zamani. Amma kuma ba wai sabo ba ne a masana’antar Kannywood domin kuwa ya daɗe ana damawa da shi matsayin mawaƙi, makaɗi, sannan kuma furodusa.
Shi wanene Bawan Mata? Me ya ja hankalin shi ya fara finafinan barkwanci? Yaushe ya fara? Me ya sa ya zaɓi barkwanci a kan mata?
Kwanan baya mujallar Fim ta tattauna da jarumin, inda ya amsa waɗannan tambayoyin da ma wasu tambayoyin a hirar sa da mujallar Fim, kamar haka:
FIM: Ka faɗa wa masu karatu cikakken sunan ka da tarihin rayuwar ka a taƙaice.
BAWAN MATA: Assalamu alaikum. Da farko dai suna na Lawal Ibrahim Gungu. An haife ni a garin Gungu ta Ƙaramar Hukumar Rimi a Jihar Katsina. Na yi karatun addini daidai bakin gwargwado, alhamdu lillah.
Shi ma na zamanin mun ɗan taɓa. Na yi makarantar firamare a wani gari da ake kira Katakam duk a Ƙaramar Hukumar Rimi ne, sannan na yi sakandare a Shudawa. Sai kuma na yi difloma a cikin garin Katsina. Mun ɗan yi ƙoƙari ba laifi.

FIM: Me ya ba ka sha’awar shiga harkar fim, musamman ɓangaren barkwanci?
BAWAN MATA: Wato ita harkar fim, abu na farko sana’a ce, abu na biyu kuma hanya ce ta isar da saƙo muhimmi ga al’umma. Saboda haka lokacin da ka ke so al’umma su fahimci wani abu, in ka bi wannan hanya ita ce mai sauƙi da saƙon ka zai isa cikin gaggawa.
FIM: Me ya sa ka zaɓi ɓangaren barkwanci, musamman ɓangaren mata?
BAWAN MATA: Wato abin da ya ke faruwa, idan ka duba za ka ga kowa da ɓangaren sa. Kuma in ka kula za ka ga mata mutane ne masu daraja, tunda ko addinin mu ya yi bayani da a tausaya masu, a kula da su da sauran su. Sannan in ka kalli namiji, duk girman sa mace ce ta haife shi. Wannan dalilin ya san a zaɓi ɓangaren mata domin in bada tawa gudunmawar ta wannan ɓangaren, sannan sauran jama’a su fahimci muhummanci da daraja da addinin Musulunci ya bai wa mata.
FIM: A wace shekara ka fara?
BAWAN MATA: E to, ba a daɗe ba sosai. Amma zan iya cewa ya kai shekara ɗaya da rabi da na fara. Domin da a masana’antar ba shi ne abin da na ke yi ba. A baya finafinai na ke shiryawa da kuma waƙa da kiɗa. Daga baya kuma tunanin wannan hidimar ta zo, da ya ke kuma Allah ya ƙaddara za a yi shi sai mu ka ci gaba da yi.
FIM: Idan na fahimce ka, a baya kai mawaƙi ne kuma makaɗi?
BAWAN MATA: Haka ne! A da ina yin kiɗa, kuma ina waƙa.

FIM: Ko za ka faɗa mana wasu daga cikin waƙoƙin ka?
BAWAN MATA: E to, waƙoƙin na yi su da dama gaskiya, sai dai wacce aka sani ba ta wuce ƙwara ɗaya ba, sauran kuma duk na siyasa, biki, suna ne da kuma sauran abubuwan da su ka yi kama da haka.
FIM: A ɓangaren shirya fim kuma fa? Waɗanne finafinai ka shirya, kuma za su kai kamar nawa?
BAWAN MATA: Waɗanda su ka fita ba za su wuce kamar guda biyu ba. Akwai kuma waɗanda ba su fita ba.
FIM: Ta wace hanya ka ke fitar da bidiyoyin barkwanci da ka ke yi?
BAWAN MATA: Gaskiya hanyoyin su na da dama. Na farko akwai shafin mu na Kannywood Exclusive a Facebook, mu na ɗora su a nan, akwai kuma canal ɗi na a YouTube, ‘Bawan Mata Comedy’, mu na ɗorawa a nan, sannan shafin mu na Kannywood Exclusive a Instagram da canal ɗin mu na Kannywood Exclusive duk mu na ɗorawa. Haka kuma masu ‘downloading’ a kwamfuta su na zuwa har inda mu ke su karɓa su je su ci gaba da rarrabawa.
FIM: Kamar yadda ka ɗauki ɓangaren mata a barkwanci, ko akwai wani ƙalubale da ka fuskanta ta ɓangaren su matan?
BAWAN MATA: To, ɓangaren su mata ban samu ƙalubale ba, sai dai a ce a ɓangaren maza. Kuma su ma mazan ba duka ba ne, waɗanda ba su fahimci abin ba ne su ke ganin kamar wani abu ne na daban, kamar ƙasƙantar da kai ne a gare mu, mu maza kenan. In da mutum zai la’akari da bayanin da na yi a baya, da na ce “duk girman namiji, mace ta haife shi”, to iya wannan ya kamata mutum ya gane abin da na ke yi ba kuskure ba ne.
FIM: A baya wani laƙabi ake kiran ka da shi, wato Agga, har yanzu ana kiran ka da sunan ko kuma Bawan Mata ya danne shi?
BAWAN MATA: Gaskiya a yanzu sunan Bawan Mata ya danne sunan da ake kira na a baya, wato Agga.

FIM: Ya alaƙar ka ta ke da sauran jaruman barkwanci?
BAWAN MATA: Alhamdu lillahi, mu na da kyakkywar alaƙa da kyakkywar fahimta da kowa. Dukkanin su abokan sana’a ne, mu na girmama juna, mu na mutunta juna, kuma sannan aikin kowa aka gayyace mu za mu je mu yi, mu ma idan mu ka yi gayyata namu aikin ana zuwa mu yi hankali kwance.
FIM: Wace hanya ku ke bi don maida kuɗaɗen da ku ke zubawa a harkar fim, ganin a yanzu babu kasuwar fim ta riga da ta mutu?
BAWAN MATA: Alhamdu lillahi, akwai hanyoyi da dama waɗanda mu ke ganin in-sha Allahu mu na da sauran dama kuma Allah ya na taimakon mu a kai. Na farko dai wannan YouTube ɗin; idan ka duba, za ka ga da dama hankalin su ya koma kan YouTube. Sannan kuma mu na da masoya da su ke yi mana alkhairi, su ke ƙaunar mu, su ke bibiyar mu, su ke kuma son abin da mu ke yi. Haka idan biki ko suna ya kama za su gayyace mu. To, ta waɗannan hanyoyin mu ke samu mu na maida abin da mu ka kashe.
FIM: Waɗanne irin nasarori ka samu a cikin wannan harka?
BAWAN MATA: Alhamdu lillahi, nasarori mun same su da dama. Don gaskiya nasarorin da na samu a wannan harka ba za su ƙidayu ba. Domin na samu alkhairai, na samu kyaututtuka bila adadin, sannan na samu yabawa daga wasu mutanen da su ka fahimci abin da mu ke yi.
Babbar nasarar da na samu a cikin hidimar ita ce masoya. Wannan shi ne abin da na ke alfahari da shi, domin shi ne ya nuna mani cewa abin da na ke yi ya na karɓuwa yadda ya kamata.
FIM: Yaya batun iyali kuma?
BAWAN MATA: Iyali akwai su. Mata na biyu.
FIM: Ka taɓa fuskantar ƙalubale ta ɓangaren iyalin ka a kan wannan sana’a da ka ke yi, musamman ɓagaren shirin ka na ‘Bawan Mata’?
BAWAN MATA: Gaskiya ban taɓa samun ƙalubale a ɓangaren iyali na ba, domin duk mutumin da Allah ya ba shi ilimin addini, za ka ga ba shi da wahalar fahimtar abubuwa.
Saboda haka lokacin da zan fara wannan harkar na samu iyali na mu ka tattauna. Daga wannan lokaci har zuwa yanzu ban taɓa samun wani ‘challenge’ daidai da ƙwayar zarra a tsakani na da su ba a game da wannan sana’a.
FIM: Faɗa mana kaɗan daga cikin manyan jaruman barkwancin da ka yi aiki da su.
BAWAN MATA: Gaskiya na yi aiki da manyan jaruman barkwanci da dama, amma zan faɗa maka wasu daga ciki. Na farko na yi aiki da Bosho, na yi aiki da Daushe, Maɗagwal, Mazaje, Jahilin Malami da dai sauran su da dama.

FIM: Wane jarumi ka fi jin daɗin aiki da shi a cikin su?
BAWAN MATA: Gaskiya abin da na ɗauki aiki idan aka zo za a yi shi, wani abu ne da ke da buƙatar kowa ya tsaya a inda aka tsaida shi. To ni duk jaruman da na ke aiki da su gaskiya ina jin daɗin aiki da su. Kuma kowannen ya na ba ni gudunmawa, sannan kowa na tsayawa a kan matsayin sa.
FIM: Ko a gaba za ka iya fitowa a finafinan da ba na barkwanci ba?
BAWAN MATA: Gaskiya a baya ba na wannan tunanin, amma dalili ya sa na fara fitowa. Domin yanzu haka akwai fim ɗin mu mai dogon zango, sunan sa ‘Lu’u-Lu’u’, wanda za mu fara sakin sa ƙarshen wata. Na fito a ciki ba sau ɗaya, ba biyu ba, ba uku ba. Kuma zan ci gaba da fitowa a finafinai ba sai na barkwanci ba, in-sha Allahu.
FIM: Mecece shawarar ka ga abokan sana’ar ka?
BAWAN MATA: Gaskiya ina da shawarwari masu yawa, musamman ga abokan mu’amalar mu. Duk harkar da ka ga Allah ya ƙaddara za ka yi, ka sani akwai hisabi a kan ta. Kiran da zan yi ga duk abokan mu’amalar mu da sauran su, kowa da kowa ya tsaya ya ji tsoron Allah; duk abin da mutum zai yi ya sani cewa Allah zai tambaye shi, don haka ya tsaida gaskiya. In-sha Allahu idan kowa ya riƙe haka, tafiyar za ta yi mana kyau, sannan kuma masana’antar baki ɗaya za ta gyaru in-sha Allahu.
FIM: Kamar yadda ka ke Bawan Mata a cikin shirin fim, haka ka ke bawan matan ka?
BAWAN MATA (dariya): Ka yi tambaya mai ma’ana. Ai ita bautar matar wata aba ce da in ka fassara ta a adabi na Bahaushe hidima ga mata kenan. Ka ga ko duk wanda ya zama ba ya hidima a gidan sa ai bai yi abin da Allah ya ce ba.
FIM: Bayan sana’ar fim, akwai wata sana’a da ka ke yi?
BAWAN MATA: Tabbas, akwai ‘business’ ɗin da na ke yi bayan sana’ar fim. Ina sana’ar jari bola. Ka san Bahaushe na cewa sana’a goma maganin mai gasa! Wannan kasuwanci kuma mun girma sosai a cikin sa. Haka kuma ya na taimaka wa ita waccan sana’a tawa ta fim.

FIM: A ƙarshe, me za ka ce wa masoyan ka?
BAWAN MATA: Alhamdu lillahi, masoya na ina alfahari da su. Sannan kuma ina yi masu fatan alkhairi a duk inda su ke. Sannan ina kira gare su, duk abin da su ka ga mun yi wanda ba daidai ba, don Allah kafin su yanke mana hukunci, su yi ƙoƙarin jin ta bakin mu. Duk abin da aka ga mun yi na laifi a yafe mana, mu ma ‘yan’adam ne. Kuma ana iya kiran mu tunda akwai lambobin waya da mu ke sakawa a cikin ayyukan mu.
—
ƘARIN BAYANIN EDITA: Shirin ‘Lu’u-Lu’u’ da Bawan Mata ya ambata, yanzu haka ana nuna shi a tashar Kannywood Exclusive da ke YouTube.