A RANAR 13 ga Nuwamba, 2023, shahararren furodusan nan kuma jarumi a Kannywood, Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya cika shekaru 57 a duniya. Wato an haife shi a 1966. Hakan ya sa ya shiga sahun dattawa.
A soshiyal midiya, mutane sun yi caa, su na taya shi murnar zagayowar wannan rana ta farin ciki a rayuwar sa.
Mujallar Fim ta tattauna da shi don jin yadda rayuwar sa ta kasance a tsawon waɗannan shekaru da kuma inda ya sa gaba.
Ga wasu daga cikin abubuwan da mu ka tsinto maku daga tattaunawar.
Godiya ga Allah:
“To a yanzu sai dai mu fara da godiya ga Allah da ya bar mu da ran mu da lafiyar mu tsawon wannan lokaci, kuma daidai gwargwado ana ci ana sha.
“Duk wata gwagwarmaya da aka yi – a faɗi a tashi, wata rana ka ji da daɗi, wata rana ka ji babu daɗi – Allah dai ya kawo mu mun ga wannan shekarun.
“Sai kuma addu’ar abin da ya ke gaba, Allah ya sa ya fi na baya alheri. Domin a yanzu da na ke cika shekaru 57 har yanzu dai mata ta ɗaya, sai dai ban san gobe me za ta haifa ba!
“Kuma ina da ‘ya’ya guda biyar. ‘Ya ta ta fari ta na gidan miji kuma ta na da ‘ya’ya biyu; ka ga ina da jikoki biyu kenan.”
Harkar Fim Da Aka Daɗe Ba A Ganin Sa A Ciki:
“To, ka san ko a baya da mu ka kafa kamfanin Iyan-Tama haka ake cewa, har yanzu kuma ba a daina faɗa ba. Ko can baya, ba a ko da yaushe ake ganin finafinan mu ba, sai mun kwana biyu mu ke shiryawa.
“A haka ne ma mujallar Tauraruwa a wancan lokacin ta yi mini take da Murucin Kan Dutse Ba Ka Fitowa Sai Ka Shirya, don sai mu shekara ban fito da fim ba. Amma idan mu ka fito, sai mu gamsar da masu kallo.
“Don haka a yanzun ma dai ana nan ana shiri a ƙarƙashin ƙasa. Zan fito da wani sabon duk da da ma a yanzu ina da wasu finafinai guda biyar da jama’a ba su gan su ba.
“Na yi su 2017 zuwa 2019; na yi fim mai suna ‘Uwar Bari’, ‘Wuta A Maƙera’, ‘Ɗan Baiwa’ ‘Wayar Hannu’, da kuma ‘Haƙƙi’. Su na nan a ajiye, fitowa ne ba su yi ba, saboda babu kasuwar fim, su kuma gidajen talbijin ba za su iya sayen fim ɗin ba. Ni kuma ban saba da YouTube ba; ina neman wanda zai iya biya na kuɗi ya je shi ya saka a YouTube ɗin ko nawa zai samu ya samu.”
Harkar Siyasa:
“Ita siyasa kowa da yadda ya ɗauke ta, don haka yadda na ɗauke ta ne ya sa aka ga abin da aka gani. Domin ita siyasa a ƙasar nan, duk yadda ka kai ga ƙwazon ka, in dai ba ka da maigida, to duk abin da ka ke da shi a banza ya ke. Don haka sai ya zama ba ni da ubangida a siyasa, duk da dai Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso na so na yi tafiya da shi, sai kuma abubuwa nawa na kai na na yau da kullum su ka hana.
“Amma ya neme ni da na zo a zauna don a yi tafiya tare, to sai ya zama a lokacin ina cikin wata sabga da ba ta ba ni damar na je ƙarƙashin sa ɗin ba.
“Amma dai tafiya irin tasa ita ce ta ke kawo wa talaka cigaba. Domin za su tsaya maka ka yi takara saboda sun isa. Su na da jama’a, su na da kyakkyawan tsari.
“Don haka a yanzu idan ya ce na zo mu yi tafiya sai na je saboda na san ya isa. Ko a baya ma harkoki ne su ka hana ni na je, amma da tun tuni ina da maigida, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. Kuma har gobe ina ganin sa a matsayin jagoran siyasa a waje na. Kamar yadda na ke ganin Malam Aminu Kano da Abubakar Rimi a siyasa haka na ke kallon sa a wannan lokacin.”

Harkar Kasuwanci:
“Duk wata harkar kasuwanci da na ke yi ina nan ina ci gaba da yi. Don ka san na gina ofishi na na harkar fim. A nan na ke yi idan harka ta zo a yi.
“Amma dai kai da kan ka ka san harkokin ba kamar da su ke ba. Situdiyo ne da mu da wajen waƙa da inda za a yi taro da sauran su, to yanzu kowa ma ya buɗe.
“Saboda haka ana samu daidai na abincin da za a ci.
“Kuma da man ina yin kwangiloli na gina gidaje. Shi ma idan ya samu ina yi. Ko irin harkar filaye duk ina yi.
“Aktin kuma babu wani furodusa da ya kira ni da har za a ga ina fitowa a fim yanzu. Don haka babu wanda ya yi mani tayi. In kuma an zo da tayin ina da ƙa’ida, ya na da tasa, sai a daidaita.”
Rayuwa Nan Gaba:
“Rayuwa ta gaba abin da ake yi na alheri za a ci gaba da yi. Makaranta ce ka sani na gina, ina son ta fara aiki, amma waɗanda za su saka hannun jari na ke nema su shigo ciki domin abin ya fi haka girma don ta zama kamar wata jami’a, ba yadda ni na ɗauko shi da farko ba.
“Wannan shi ne ya sa makarantar harkar fim da na gina har yanzu ba ta motsa ba, amma komai da akwai a ciki. Ina son a faɗaɗa ta ta fi yadda ta ke a yanzu.
“Na biyu kuma, a yanzu mu na ta ƙoƙarin mu samar da labarin (fim) da ba a taɓa yin kamar sa ba domin na nemo waɗanda za su ɗauki nauyi. Ko ba kuɗi na ba ne a yi domin a shiga manyan kasuwanni na zamani da su ke ci a yanzu a harkar fim ta duniya, ba irin namu na gida ba.
“Don haka ina son na yi babban fim wanda zai goga da finafinai na duniya. Wannan shi ne abin da na sa gaba, kuma idan Allah ya yarda in ana raye za mu kai ga cimma burin mu.”
Waiwaye:
Sanadiyyar shigowar Iyan-Tama harkar fim ita ce haɗuwar sa ta farko da jarumi kuma furodusa Ɗan Azimi Baba Ceɗiyar ‘Yangurasa a shagon wani abokin sa.
Ya fara da shirya fim mai suna ‘Bakandamiyar Rikicin Duniya’ a 1996. Tun daga nan ya ci gaba da bada gudunmawa ga industiri wajen yin finafinai masu ma’ana, waɗanda kuma su ka dace da yanayin al’adun mu da addinin mu.
Kamfanin sa na Iyan-Tama Multimedia Nigeria Limited ya kasance zakaran gwajin dafi a irin kamfanonin da su ka yi tashe a Kannywood. Shi ne wanda ya fara kawo na’urar ɗaukar hoto mai suna PSR-220 wadda a lokacin babu irin ta. An yi amfani da ita wajen ɗaukar waƙar fim ɗin ‘Badaƙala’.
Alhaji Hamisu ne ya fara riƙe muƙamin Shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Arewacin Nijeriya (Arewa Film Producers Association of Nigeria, AFPAN) wadda ita ce ta farko irin ta a Kannywood, kuma ta taimaka gaya wajen saisaita harkar fim a farkon fara ta.
Iyan-Tama ya samu kyaututtuka sama da 40, wasu na ƙasa-da-ƙasa ne, kamar Amurka, Kanada, Indiya, da kuma na cikin gida.
Ya taɓa yin takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar National Democratic Party a shekarar 2007.

Finafinan da ya samar su ne:
Badaƙala (1997)
Ƙilu Ta Ja Bau (1997)
Saudatu (1998)
Gashin Ƙuma (2000)
Haƙuri (1999)
Ƙwai A Baka (1998)
Na San A Rina (1998)
Buri
Ƙin Gaskiya
Mara Gaskiya
Alƙawari
Wata Rana
Fallasa
Tsintsiya
Kurkuku,
da sauran su.