ALLAHU Akbar! Bayan rasuwar Alhaji Yusuf Barau, mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin wasu daga cikin abokan sana’ar sa game da yadda wannan rashi da ya riske su. Mutanen, waɗanda su ka yi hulɗa ta ƙut da ƙut da marigayin a Jihar Kaduna, sun yi ƙarin haske game da yadda su ka yi rayuwa da Yusuf Barau, wanda Allah ya yi wa rasuwa a jiya Laraba, 15 ga Satumba, 2021 a Kaduna.
Ga abin da su ka faɗa wa mujallar Fim a cikin alhini:
MALAM MUSA MOHAMMED ABDULLAHI:
To, Abba ka ga yanzu ba zan iya yin wani bayani ba a cikin jimami. Yusuf Barau cikakken amini na ne tun mu na ƙanana. Tare mu ka yi Teachers College. Har Allah ya karɓi ran sa duk tare ake. Kusan a Kaduna, ko ma ina ne, duk wanda ya san shi ya san ni, wanda ku ma ya san ni ya san shi. Tun kafin mu yi aure dukkan mu gaba ɗaya, har ya kasance yanzu mu na da iyalai ‘ya’ya da yawa; ina da kusan ‘ya’ya ashirin. To Malam Abba, sai dai mu ce Allah ya jiƙan shi da rahama.
AL-AMIN CIROMA:
Wallahi wannan rashi dai za mu iya cewa masana’anta ta yi babban rashi. Domin in aka lura kamar shi Yusuf Barau kusan shi ne za a iya cewa jarumi na farko a masana’anta, wanda tun kafin a ce za a yi finafinai na bidiyo da ke sayarwa a yanzu Yusuf Barau ya yi finafinai da dama. Zan iya tuna wani fim wanda har da ‘yar’uwa ta a ciki, Turawa ne su ka zo daga Jamus aka yi fim ɗin tun zamanin Babangida, har aka yi ‘launching’, to ina iya sanin wannan ‘project’ ɗin da Yusuf Barau ya yi shi ne jarumi. Ita kuma ‘yar’uwar tawa tare su ka yi, wanda sanadiyyar hakan har ita ma ta samu ɗaukaka, har ta yi aure a can ƙasar su.
Tun kafin a ce za a yi irin su ‘Turmin Danya’ da sauran su. Aka zo kuma aka yi ‘Shamsiyya’, wanda shi ne ‘first horror film’ da aka yi a Kannywood, wanda kuma su ne jarumai a ciki.
Yusuf Barau mutum ne kamili. Mutum ne mai son jama’a. Ba za ka taɓa ji an ce ga wani can ya yi faɗa da Yusuf Barau ba. Don haka an yi babban rashi gaskiya, sai dai mu yi ta fatan abubuwan da ya yi na alheri su raka shi. Allah ya gafarta masa.
ABDULLAHI MAIKANO USMAN:
Wato tsakani da Allah ni a wuri na an yi rashi ne kala uku. Na farko, an yi rashi ne a matsayin ɗan’uwa na Musulmi, wanda shi ne babban rashi. Allah ya jiƙan shi da rahama.
Na biyu, a matsayin wanda ya yi fice a harkar finafinan Hausa a Jihar Kaduna da kuma arewacin ƙasar nan baki ɗaya, mun rasa ɗan’uwa abokin sana’a. A rayuwa ta a matsayi na na furodusa, Yusuf Barau shi ne ya yi sanadiyyar yin fim ɗi na mai suna ‘Zumuɗi’, wanda fim ne da ya yi fice. Shi ya bada shawarar yin wannan fim ɗin.
Saboda haka a matsayin abokin sana’a, nan ma mun yi asarar ɗan’uwa. Mu na roƙon Allah ya sanya lahirar sa ta fi duniyar sa da mu baki ɗaya.
Na uku, a matsayin shi na yayan mu, wanda ya ke ya ba mu shawarwari a wannan harka tunda ya riga mu shigar ta. Ina roƙon Allah subhanahu wa ta’ala ya nauwara masa kabarin sa, ya sa Aljanna ce makomar sa.
Kuma Yusuf Barau ya na ɗaya daga cikin mutanen da na sani a industiri, wanda ba magulmata ba ne.
Ni ban taɓa ganin wata ɗabi’a ta hassada tattare da Yusuf Barau ba. Gaskiya duk wanda aka yi masa shaida da son ɗan’uwan sa da son cigaban ɗan’uwan sa, gaskiya ya samu shaida mai kyau. Allah ya yi masa kyakkyawar sakayya, ya kuma shirya masa zuri’a.
ADAMU BELLO ABILITY:
Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Haƙiƙa mun yi babban rashi. Malam Yusuf Barau yaya na ne, mun yi aiki kusan shekara talatin tare da shi. Wallahi mutum ne mai ƙwazo wurin aiki, mutum ne mai haƙuri, mai kuma barkwanci.
Gaskiya mun yi babban rashi. Sai mu yi masa addu’ar Alllah ya gafarta masa, ya kuma yafe masa. Allah ya sa ya huta.
Wallahi na samu labarin rasuwar sa cikin ruɗani. Allah ya sa ya huta. Mu kuma in tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani.

MAGAJI SULAIMAN:
Allahu Akbar! Idan akwai wanda rashin zai shafa, ɗaya, biyu, ina cikin na uku saboda Yusuf Barau ɗan’uwa ne kuma yaya na ne, gaskiyar magana, domin ɗan Zariya ne kusan ga gida ga gida.
Kuma shi ne mutum na biyu bayan Abdullahi Maikano, a lokacin da zan fara fim ɗi na, ‘Yarima Ɗan Sarki’, shi ne wanda na samu kuma ya sa ni a hanya.
Wallahi Yusuf Barau mutum ne nagari. Don abubuwan da ake yi yanzu da za ka ga yara ‘they are after money’. Shi a kullum ya na yi yadda za a iya, domin gobe a yi ko da shi ko ba shi za ka iya yi. To ka ga shi ɗan wasa ne, kuma marubuci har ila yau, ya kuma zo in ana aiki za ka ji ya na ga gyaran da za a yi, ga gyaran da za a yi don a samu nasara.
Ina yi masa fatan Allah ya yi masa rahama, ya kuma gafarta masa.
FATIMA JAFARU (GUDIDI):
Gaskiya wannan rashi ya zo mana da ‘shock’. Kuma ka san idan lokaci ya yi babu magani. Allah ya gafarta masa.
Alhaji Yusuf Barau ya na ɗaya daga cikin waɗanda su ka ɗauke ni aiki, kuma ya na cikin waɗanda su ka yi min intabiyu lokacin da aka ɗauke ni aiki.
Abin da zan iya tunawa game da shi, shi mutum ne mai son wasa; in ba ka iya abu ba a kan aiki zai kwantar da hankalin sa ya koya maka, ya kuma nuna mana in lokacin wasa ya yi a yi wasa, in lokacin aiki ne a yi aiki.
Kuma ya na da gaskiya. Ga addini. Ni abin da zan iya cewa Allah ya jiƙan shi, ya kuma kai haske kabarin sa. Idan tamu ta zo kuma, Allah ya kyautata makwancin mu.
SANI IDRIS KAURU (MOƊA):
Alhamdu lillahi! Bisa abin da Allah ya sanar da mu a Alƙur’ani, ya ce, “Kullu nafsin za’ikatul maut”, mun riga da mun san akwai ta. Amma ba ka sanin rana ko lokaci.
Saboda haka jiya na je asibitin Barau Dikko, aka ce min an gan shi a asibitin, ya zo a duba shi, to sai ba a samu damar yin hakan ba, sai aka ce ya wuce wani asibitin. Wannan asibitin da ya wuce shi ne ban sani ba. Don yau da Malam Musa Mohammed Abdullahi, aminin sa na rayuwar sa da su ka taso tare, ya kira ni a waya ya ke sanar da ni da abin da ya faru,farko abin da na fara dubawa abu biyu ne.
Na farko na san ya na da cutar ciwon suga kamar yadda na ke da shi. Na biyu shi ne bai kwanta kamar yadda ni na kwanta ba, kuma abin bai yi masa tsanani kamar yadda ya yi min ba. Allah cikin ikon sa, ina ganin kamar ya na ganin abin ya ɗaga masa ya je asibiti a duba shi a ga abubuwan da ke damun sa. To ganin haka shi ya sanya ya tafi asibiti.
Kamar yadda na faɗi cewa mutuwa mun san da ita, amma ba mu san lokaci ba, ba kuma mu san wace rana za ta zo ba, to irin wannan da zai zo maka kwatsam, ya fi sa ka girgiza. Misali, kamar ni lokacin da na kwanta, an yaɗa labarin na rasu, amma a yanzu da zan rasu ba za a ji abin kamar yadda aka ji a wancan lokacin ba, saboda an saba da ƙarya cewa ai ya rasu, da sauran su. Sai in jama’a sun gaskata rasuwar sannan za a yarda.
Amma ka ga kamar nashi, ta zo ne kawai kwaf a lokaci guda. Saboda haka irin wannan rasuwa ya fi girgiza mutane.
Alhamdu lillahi, a yanzu ba kowa ne ya san shi ba, tunda a lokacin da ya yi tashen sa an daɗe, ba kamar yanzu da za a kira shi ya yi ɗaya biyu ba. Kuma ga shi ni da shi duk ma’aikata ne na gwamnati, ba kowa ya san mu da aikin gwamnati ba, an fi sanin mu a fagen shirin fim. Amma shi ya yi ritaya shekara biyu zuwa uku da su ka wuce.
A gaskiya ko a ofis, ba don yanzu ya rasu na ke faɗi ba, halin mutum nagari ake faɗi ko da bayan ba shi. To, amma wannan bawan Allah a lokacin da na san shi ido da ido, aiki ne ya dawo da ni daga ƙaramar hukuma na zo nan ofishin a matsayin ma’aikaci, ni dai ba zan ce ba, ban sani ba ko mun taɓa samun saɓani da shi kusan shekara talatin da su ka wuce baya. Amma abin burgewa, abin da ni ba zan mance ba a lokacin nan a 1994, 1995 finafinai irin namu na Hausa na Kannywood bai yi nisa ba, bai ma je ko’ina ba, ba a ma san shi a ƙasar Hausa ba. Shi ne mutum na farko da ya fara gayyata da na fara zuwa duk wasu harkokin gidan talabijin na NTA Kaduna, wani shiri da marigayi Umar Hassan, Allah ya gafarta masa shi ma, a wannan lokacin ana cewa shirin ‘Zamani’. Wannan mutumin shi ya fara sa ni. Ba wai shi ya koya min wasannin kwaikwayo ba, domin na fara tun ban zo Kaduna ba, ban ma san zan san shi ba, ni na fara a 1979, ka ga shekara 15 kenan zuwa 16 a wannan lokacin Allah ya haɗa ni da shi.
A gaskiyar magana na ji daɗin yadda mu ka haɗu da shi. Zan iya tunawa, a wannan lokacin aka ce za a yi wannan fim ɗin mai suna ‘Taskira’, ya gayyace ni na fara yin wannan, na fito a sanƙira. Sai kuma aka yi ‘Komai Tsawon Dare’. A wannan lokacin na fara fita. Aka zo aka shirya min fim nawa na musamman wanda ni ne jagoran fim ɗin, ‘Ɗan Duniya’, wanda Abdullahi Sa’idu Bello shi ya yi.
To ka ga wannan bawan Allah Yusuf Barau shi ne jigon ɗora ni a kan waɗannan harkoki na finafinai. A yau bawan Allah ba shi, kuma ina kyautata zaton na ɗaya da cikin mutum na farko da na fara turawa a soshiyal midiya, bayan Musa Abdullahi ya kira ni.
Mun yi ƙoƙari mu ga cewa an yi jana’izar sa a nan Kaduna saboda masoya, amma haka bai yiwu ba.Ina yi masa fatan Allah ya jiƙan shi da rahama, ya kuma sa Aljannar Firdausi ce makomar sa.
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved
www.fimmagazine.com