ƘUNGIYAR ciyamomin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na jihohin Arewa 19 da Abuja sun miƙa saƙon ta’aziyyar su ga uwar ƙungiyar ta ƙasa da ‘yan Kannywood da kuma iyaye da iyalan marigayi Aminu S. Bono.
A cikin takardar ta’aziyyar da su ka fitar a jiya Litinin da sa-hannun shugaban ƙungiyar ciyamomin, Alhaji Haruna Mohammed Godowoli, ƙungiyar ta ce, “Mun yi baƙin cikin jin labarin rasuwar ɗaya daga cikin mu, wato Aminu Suraj Bono. Don Allah a karɓi ta’aziyyar mu, a madadin Rasdan mu na jihohi, kuma ku sani cewar mu na yi wa dukkan MOPPAN da Kannywood da iyalan sa addu’o’i a wannan lokaci na tsananin jimami.
“Mun ji daɗin sanin da kuma yin aiki tare da Aminu Suraj Bono ta dalilin wannan ƙungiya ta MOPPAN da Kannywood, kuma za mu riƙa tunawa da shi ta dalilin kirkin sa abin burgewa, da kyakkyawar tarayya, halayyar sa, da gudunmawar sa ga cigaban wannan hamshaƙiyar masana’anta mai girma, MOPPAN/Kannywood, ba Kannywood kaɗai ba, har da abokan sa da ke zagaye da shi, amma yadda ya ke da iyawar ban-mamaki don kawo farin ciki da annashuwa ga ɗaukacin arewacin Nijeriya ta dalilin finafinan da ya yi aikin su a matsayin darakta.
“Wata shaida game da ta halin Aminu Suraj Bono ita ce tasirin da ta yi mai ɗorewa a rayuwar da dama da ɗaliban sa da ya koya wa Alƙur’ani a matsayin sa na malamin su.
“A madadin ciyamomin jihohi na MOPPAN, mu na miƙa ta’aziyyar mu gare ku. Allah ya sa rayuwar da kyautatawar Bono su zama tushen ƙarfafa zuciya da zaburarwa ga masana’antar da dangin sa.
“Mu na jin daɗin cewa ruhin sa zai rayu ta hanyar tasiri mai ɗorewa da ya yi wa duk wanda ya yi hulɗar da shi kai-tsaye ko a fakaice.
“Har ila yau, mu na ta’aziyyar rashin sa, kuma mu na aika wa kowa da kowa soyayya da goyon bayan mu a wannan lokaci na ƙalubale.
“Allah ya sa Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare shi, amin.”