INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa tsohuwar shugabar ƙungiyar furodusoshi mata ta farko, Hajiya Umma Ali, rasuwa.
Ta rasu a asibitin Premier da ke Kano da yammacin nan.
Ɗazu da rana aka garzaya da ita asibitin saboda rashin lafiya.
Za mu kawo ƙarin bayani anjima.
Allah ya rahamshe ta, ya sa Aljanna ce makomar ta, amin.