WANI fitaccen ɗan siyasa a Kano, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim A.A. Zaura, ya sha alwashin gina wa masana’antar Kannywood tsangayar shirya finafinai, wato ‘film village’, a jihar Kano, a yunƙurin sa ya jawo ‘yan masana’antar a jika.
Ɗan siyasar ya na ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamnan jihar.
Labarin hakan ya fito ne daga bakin jarumi kuma mawaƙi T.Y. Shaban a wurin taron tantance matasan da su ka shiga wata gasar waƙa ta bidiyo wadda gidauniyar A.A. Zaura ta shirya domin tallafa wa matasa ta hanyar waƙa.
T.Y. Shaban ya ce, “Wannan wata dama ce da aka buɗe tsakanin matasa maza da mata har ma da masu buƙata ta musamman ta hanyar shirya waƙa da za a ɗauki bidiyon da bai wuce tsawon minti ɗaya da rabi ba.
“Ganin yadda matasa a yanzu su ke bai wa ɓangaren nishaɗi muhimmanci ya sanya aka kawo shawarar fito da wannan gasa irin ta ta farko da za a bai wa waɗanda aka zaɓa kyaututtuka daga na ɗaya har zuwa na 30 sakamakon yadda matasa su ka shiga gasar su kimanin 3,000.”
Jarumin, wanda ya na ɗaya daga cikin alƙalan gasar, ya bayyana cewa su na lura da wasu ƙa’idoji guda tara waɗanda sai mutum ya cika su sannan zai samu nasara.

“Kaɗan daga cikin abubuwan da mu ke dubawa wajen zaɓen sun haɗa da yadda aka ɗauki hoton waƙar da yanayin kayayyakin da mutum ya sanya tare da nuna yadda ɗan takarar ya shiga jam’iyyar APC, da sauran su.”
Da mujallar Fim ta tambayi jarumin idan akwai wani abu wanda zai kawo wa wannan masana’anta cigaba ta hanyar wannan gidauniya, ba wai iya saka gasar waƙa ba, sai ya amsa da cewa, “Akwai ƙoƙarin da mu ke yi tare da shugaban wannan gidauniya, Alhaji Abdulsam Abdulkarim, wajen fito da tsare-tsare da zai taimaka wa wannan masana’anta, da ma masu sha’awar shiga cikin ta ta hanyar gina tsangayar shirya finafinai domin samar da kuɗin shiga da ƙarin wurin aikin yi ga matasa ba tare da sun jingina da kowa ba.”
Cikin abubuwan da za a bayar ga waɗanda su ka samu nasara sun haɗa da mota, mashin mai ƙafa uku, wato Adaidaita Sahu, mashin mai ƙafa biyu, keken hawa da kuma kuɗaɗe masu yawa.
Tantancewar ta na gudana ƙarƙashin jagorancin fitaccen darakta Ali Gumzak tare da alƙalai da su ka haɗa da darakta Hafizu Bello da T.Y. Shaban da kuma wasu masu tantancewar na ɓoye.
Ana sa ran za a kammala wannan tantancewar nan ba da jimawa ba.
Idan kun tuna, gwamnatin Muhammadu Buhari ta taɓa ɗaura aniyar gina ‘film village’ a Jihar Kano, wanda hakan ya faranta ran dukkan ‘yan masana’antar Kannywood, domin an hango cewa ƙudirin zai samar wa da matasan Arewa aikin yi.
To amma ƙudirin ya samu tasgaro saboda wasu malamai da sauran jama’ar jihar ba su ba lamarin goyon baya ba.
