“Ba ta bar talakawa ba mutuwa ta yanke talaucin su,Ta kan bi sarakai ma mutuwa ta raba su da mulkin su,Da ido na na ga mutuwa ta ɗauke ma’azurta.Uuhum wayyo kai na, mutuwa riga ce ba ta fita.”
BAITIN waƙar mutuwa kenan ta shahararren mawaƙin yabon Manzon Allah (s.a.w.), Sharif Rabi’u Usman Baba, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar 9 ga Mayu, 2019 bayan wata gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu a gidan sa da ke unguwar Janbulo a cikin garin Kano.
Marigayin, mai shekaru 52 a duniya, ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya 13.
Kafin rasuwar sa dai shi ne shugaban ƙungiyar sha’irai da ake kira Shu’ara’ul Islam.
Rasuwar sa ta jijjiga duniyar Musulmi baki ɗaya, domin kuwa Sharif Rabi’u Usman Baba ya zama fitaccen mawaƙin Annabi sakamakon irin salon da ya zo da shi da kuma tafiya da zamani. Irin salo da jigon da ya ke amfani da shi wajen faɗakarwa, ilimantarwa ta hanyar waƙoƙin sa ya zamo abin karɓuwa a wajen jama’a. Don haka babu wani kokwanto shi wani jigo ne a cikin waɗanda su ka kawo wa ɓangaren waƙoƙin Musulunci juyin-juya-hali.
Tauraruwar Rabi’u Usman Baba ta fara haskawa ne tun cikin shekarar 1985, kuma ya zuwa 1998 ya yi shaharar da babu wani sha’iri da za a haɗa shi da shi a fagen waƙa.
Ya yi waƙoƙi da ba su da adadi, amma dai waƙar da ta fara fito da shi tun daga farko ita ce, ‘Dukkan Mai Matsayi Wajen Ilahu Ba Zai Kai Ka Ba’.
Fitowar wannan waƙa ta sauya alƙiblar matasa da yara ƙanana, domin kuwa a lokacin da waƙar ta fi waƙoƙin da su ke tashe kuma su ka fi karɓuwa ga matasa da yara su ne na Indiya da na Sudan, waɗanda ana sauraren su ne ba don ana fahimtar abin da su ke faɗa ba sai dai son nishaɗi kawai. Amma fitowar wannan waƙar ta Rabi’u Usman Baba da sauran waƙoƙin sa da su ka biyo bayan ta ya kawar da waƙoƙin Indiya da na Sudan daga bakin matasa da ƙananan yara, don haka duk lokacin da za ka ji yara su na waƙa don nishaɗi sai ta yabon Manzon Allah. Kuma hakan ya sa matasa da dama su ka rungumi ɗabi’ar shirya waƙoƙin yabon Manzon Allah.
Kafin wani lokaci sai ga shi a birnin Kano da sauran jihohi an samu masu yabon Manzo ba su da adadi.
Tafiya da zamani ta sa Sharif Rabi’u Usman Baba ya daɗe ya na jan zaren sa, domin kuwa a farkon waƙar sa ya fara ne babu kiɗan bandiri, amma ganin Ƙadirawa da su ke yin waƙa da bandiri su na karɓuwa sai shi ma ya juya ya shigar da bandiri cikin waƙar sa, duk kuwa da cewa a lokacin ya sha suka a wajen Tijjanawa da su ke ganin Ƙadirawa ne su ke kaɗa bandiri; a tafiyar Tijjaniya babu kiɗan bandiri. Amma dai ya tafi a hakan tare da ba su amsar da ya ke ganin ita ce hujja a gare shi.

A lokacin da kiɗan fiyano ya fara tashe, nan ma Sharif Rabi’u Usman Baba bai yi ƙasa a gwiwa ba, sai ya ɗauki salo don ganin kada waƙoƙin finafinan Hausa da su ke tashe a lokacin su rufe irin nasa. Don haka shi ma sai ya fara waƙa da kiɗan fiyano inda a nan ma ya yi ta samun suka, sai dai ya kare kan sa da waƙoƙin Larabawa na yabon Manzo da su ke yi da kiɗa. Ya nuna cewar waƙar sa da fiyano a duniyar Musulunci abu ne karɓaɓɓe, in dai za a bi tsarin da ya dace.
Marigayin mutum ne da ya san ’yancin sa, don haka bai yarda zama cikin rashin ’yanci ba, domin kuwa an yi wani lokaci da duk shaharar da mawaƙi ya yi to ’yan kasuwar da su ke buga kaset a Kasuwar Ƙofar Wambai su ke kallon su ne kawai su ka ɗaga shi. Amma shi da su ka kawo masa wasu dokoki ya ga ba zai amince da su ba sai su ka raba hanya. Sai ya buɗe ‘Tsumagiya Studio’ a unguwar Gwammaja, wanda duk mutumin da ke son waƙoƙin sa ya je can ya saya saboda ‘yan kasuwa sun daina buga waƙoƙin sa.
Hakan bai sa sha’irin ya koma baya ba, sai ma shaharar sa ta yi gaba.
Haƙiƙa Malam Rabi’u mutum ne da ya yi rayuwar sa cikin shahara kuma har ya koma ga Allah tauraron sa bai dusashe ba. Domin kuwa da aka bayyana rasuwar sa a soshiyal midiya, sai masu hulɗa da shafuka su ka yi ta saka hotunan sa da kuma rubuce-rubuce na alhini da miƙa ta’aziyya ga al’ummar Musulmi a game da rashin sa.
Lallai duniyar Musulmi ta yi rashin babban mawaƙin Annabi. Kuma za a daɗe tarihi bai manta da Sharif Rabi’u Usman Baba ba, musamman ‘Tsumagiya’, ‘Isra’i’, ‘Imamul Mursalina’, da sauran ɗimbin waƙoƙin sa.
Mu na fatan Allah Ya jiƙan sa, Ya kai rahama kabarin sa. Allah Ya albarkaci zuriyar sa, Ya bai wa dukkan Musulmi haƙurin jure wannan babban rashin da aka yi, amin.
![]()







