MATASHIN editan finafinai a Kannywood, Hafiz Hamisu (SB), shi ma ya shirya tsaf don bankwana da kwanan shago.
Za a ɗaura auren sa da sahibar sa, Iƙilima Tasi’u (Babyn Baby), a ranar Juma’a, 24 ga Nuwamba, 2023 da misalin ƙarfe 2:00 na rana a masallacin Juma’a da ke Kabala Costain, Kaduna.
Bayan ɗaurin auren za a yi walima a Layin Samba Shehu, Malali, Kaduna.
Haka kuma akwai Yammacin Abokai, wanda biki ne na musamman na ango da abokan sa da za a yi da safe a ranar Juma’a kafin lokacin ɗaurin auren.