• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Fim ɗin ‘Zo Mu Zauna’ ne silar ɗaukaka ta – Saratu Abubakar

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
August 19, 2022
in Taurari
1
Saratu Abubakar

Saratu Abubakar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DUK wanda ke kallon shiri mai dogon zango na ‘Zo Mu Zauna’ a tashar YouTube ta Rariya ba zai manta da Saratu Abubakar ba, wato Hajiya Baraka, saboda irin rol ɗin da take takawa na babbar mace, duk kuwa da kasancewar ta budurwa mai ƙarancin shekaru. Jarumar ta bayyana cewar fim ɗin ya zama wani mataki na ɗaukaka a gare ta, domin duk inda ta je ana kallon ta a matsayin babbar mace kuma ana mutunta ta, duk da cewar rol ɗin da ta fito na rashin mutunci ne.

Mujallar Fim ta tattauna da Saratu a kan tarihin ta da yadda aka yi ta shigo Kannywood.

FIM: Ki ba mu tarihin rayuwar ki da yadda aka yi ki ka shigo harkar fim.

SARATU ABUBAKAR: To ni dai suna na Saratu Abubakar, kuma Hajiya Baraka a cikin shirin ‘Zo Mu Zauna’ na tashar Rariya da ake haskawa a YouTube.

Ni asali na ‘yar jihar Neja ce, a garin Suleja. An haife ni a 1993. A nan na tashi na girma, na yi karatu na na firamare da sakandare, kuma yi NCE a Minna.

FIM: Ya aka yi ki ka samu kan ki a harkar fim?

SARATU ABUBAKAR: To, na fara harkar fim tun a 2014, kuma fim ɗin da na fara yi shi ne ‘Hajiya Babba’. Sai dai a lokacin ban sa wa harkar fim ɗin himma ba saboda ina karatu, shi ya sa na ɗan dakatar.

Saratu Abubakar (a dama) tare da su darakta Ishaq Sidi Ishaq

To daga baya da yake na dawo ina ci gaba da karatu a Kano shi ya sa na ga bari na ci gaba da yi, don haka da na dawo na yi ‘Matar Mamman’ da kuma ”Ya’yan Mage’, amma duka dai ba wasu sinasinai na yi ba da yawa a cikin su.

FIM: Ko ya aka yi ki ka samu shiga fim ɗin ‘Zo Mu Zauna’ har ki ka zama jarumar fim ɗin?

SARATU ABUBAKAR: To yadda na samu kai na dai shi ne akwai wani da mu ke mutunci da shi, ya ce zai zo inda na ke mu gaisa. Kuma da ya zo sai na gan shi tare da darakta Ishaq Sidi Ishaq. To ganin da na yi masa a lokacin sai na nuna masa na ji dali don ban taɓa ganin sa ba sai dai a fim. Sai na faɗa masa ai ni ma ina yin fim, har a cikin ‘Kwana Casa’in’ na fito.

To sai ya ce akwai fim ɗin da aka ba shi aka ce ya nemo masu aikin. To da haka na samu shiga har na zamo maman Nadiya, wato Hajiya Baraka kenan.

FIM: Ko ya ki ke kallon kan ki a matsayin Hajiya Baraka a cikin ‘Zo Mu Zauna’?

SARATU ABUBAKAR: Gaskiya abin ya na burge ni, saboda ita Hajiya Baraka mata ce marar mutunci, don haka duk da ba hali na ba ne abin ya na burge ni, saboda na bayar da abin da ake so a fim ɗin, har ma wasu su na ganin kamar hali na ne na ke nunawa a fim ɗin; kuma ba haka ba ne, fim ne kawai.

FIM: Ko ya za ki kwatanta ‘Zo Mu Zauna’ da kuma waɗanda ki ka yi a baya?

SARATU ABUBAKAR: A gaskiya, duk da yake a baya na taɓa fitowa a matsayin matar aure, amma babu wani fim ɗin da na samu ɗaukaka kamar ‘Zo Mu Zauna’ saboda matsayin da aka ba ni a fim ɗin, domin ka ga na fito a babbar mace mai aure, har ta aurar da ‘yar ta, kuma ni ban taɓa yin aure ba a matsayi na na budurwa To wani lokacin ni da kai na idan na kalli fim ɗin sai na ji ni wani irin. Amma dai ina alfahari da fim ɗin saboda shi ne ya sa na samu ɗaukaka duniya ta san da ni, don haka ina alfahari da shi.

Saratu Abubakar: “Wasu na ganin rashin mutunci kamar hali na ne, amma fim ne”

FIM: Menene saƙon ki na ƙarshe?

SARATU ABUBAKAR: To, ni dai abin da zan ce shi ne masu kallon shirin su ci gaba da kallon tashar Rariya TV a YouTube domin su riƘa ganin mu, kuma su riƙa yi mana addu’a da ba mu shawara. Mu na alfahari da irin yadda su ke nuna kulawar su a gare mu.

Loading

Tags: Ishaq Sidi IshaqjarumaKannywoodRariya TVSaratu AbubakarZo Mu Zauna
Previous Post

Buri na a gyara lafuzzan da ake furtawa a yabon Annabi – Ummi Burdatu

Next Post

Siyasar Kannywood: Ana zargin T.Y. Shaban da Ahlan da cinye tallafin A.A. Zaura

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
TY Shaban (a hagu) da Shariff Aminu Ahlan su na kamfen ɗin A.A. Zaura a Kano

Siyasar Kannywood: Ana zargin T.Y. Shaban da Ahlan da cinye tallafin A.A. Zaura

Comments 1

  1. Abdullahi GAMAWA says:
    3 years ago

    Fatan Nasara..
    Ina miki fatan ki samu miji kiyi Aure..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!