ALLAHU Akbar! A ranar Asabar, 14 ga Oktoba, 2023, Allah ya ɗauki ran mahaifiyar furodusa a Kannywood, Hamisu Bawasa.
Mahaifiyar tasa, Malama Fatima Muhammad, ta rasu a gidan ta da ke ‘Yantukwane, Tudun Wada, Kaduna, bayan ta yi sallar asuba, ta na zaune a kan sallaya ta na lazumi.
Bawasa ya shaida wa mujallar Fim abin da ya faru, ya ce, “Lafiya lau ta kwanta, kuma lafiya lau ta tashi da asuba, ta ɗora ruwan zafi a wuta, sannan ta yi alwala, ta yi sallar asuba. Bayan ta idar da sallan ta na lazumi rai ya yi halin sa.
“Wannan ruwan da ta sa a wuta, ashe ruwan da za a yi mata wanka da shi ne, ba na wankan yara ba.”

Marigayiyar, mai kimanin shekaru 57 a duniya, ta rasu ta bar ‘ya’ya shida da jikoki 24. Hamisu shi ne ɗan ta na farko.
An yi jana’izar ta da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ‘Yantukwane, daga nan aka kai ta gidan ta na gaskiya.
Wakilin mu ya ruwaito cewa tsakanin ta da mijin ta shekara ɗaya da wata huɗu kenan.
Wasu daga cikin waɗanda su ka je ta’aziyya sun haɗa da Abdullahi Maikano Usman, Dikko Yakubu, Sabi’u Gidaje, Haruna Gidaje, Nura MC Khan, Yaros Khan, Abubakar Hunter, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Ɗanjummai CV, Nura Obi, Abdul SD, Najeeb Marubuci, ‘yan kamfanin Wassh Production, Ibrahim Belsha, Aliyu A. Lion, Asabe Madaki, Zainab Baka, Ruƙayya Nasarawa, Bilkisu Kawo, da Anisat Ahmad.
Allah ya jiƙan Mama Fatima da rahama, ya sa mutuwa hutu ne a gare ta.isu