• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ghali DZ ya zama shugaban gidan talbijin na Hijrah

by MUKHTAR YAKUBU
October 12, 2025
in Labarai
0
Ghali DZ ya zama shugaban gidan talbijin na Hijrah

Ghali El-Abdallah DZ

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Hukumar Gudanarwa ta gidan talbijin na Hijrah ta tabbatar da naɗin Ghali El-Abdallah DZ a matsayin sabon Manajan Darakta na tashar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar gidan talbijin ɗin ta raba wa manema labarai, inda ta ce sun yi naɗin ne saboda irin gwagwarmayar da Ghali ya yi a gidajen rediyo da dama da kuma masana’antar Kannywood.

Ta ce wannan dalilin ya sa suka tabbatar da yana muhimmiyar gudunmawa da zai bai wa tashar Hijrah TV a irin wannan lokaci.

Ghali dai fitaccen mawaƙi ne,  furodusa kuma jarumi.

An haife shi a unguwar Durumin Zungura da ke cikin birnin Kano a shekarar 1978. Ya yi makarantar firamare a Kwalli kuma ya yi Ƙaramar Sakandare a Sabuwar Ƙofa, sai Babbar Sakandare a Kwalejin Rumfa, Kano.

Ya ci gaba a Kwalejin Sa’adatu Rimi inda ya yi NCE, sai kuma ya tafi Jami’ar Bayero inda ya samu Babbar Difloma a fannin aikin jarida.

A ɓangaren aiki kuwa, Ghali  ya yi aiki a gidan rediyon Freedom FM da gidan rediyon Rahama FM da gidan rediyon Arewa, sai Kannywood Series TV da kuma Hijira TV.

A Kannywood kuma Ghali ya kasance komai da ruwan ka, inda ya fara da waƙoƙin tallace-tallace da na wayar da kai. Sai kuma shirin sa mai farin jini na “Dandalin Fasaha” inda yake hira da mawaƙa da ‘yan fim.

Bugu da ƙari shi ne marubuci kuma jagoran shirya wasan kwaikwayo na ‘Birnin Dala’  a Dala FM, sai kuma wasan kwaikwayo na ‘Ƙasar Jallaba’ a tashar Arewa FM wadda daga baya aka yi fim ɗin wasan kwaikwayon da sunan ‘Mai Martaba’, fim ɗin da ya shiga jerin finafinan da suka wakilci Nijeriya a gasar Oscars a Amurka.

Loading

Tags: Ghali DZHijrah TVnaɗi
Previous Post

Addu’ar uku: Marubuta sun yi dandazo wajen ta’aziyyar Hauwa Lawan Maiturare

Next Post

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na – Bilkisu Yusuf Ali

Abin da ya sa na fi shaƙuwa da marigayiya Hauwa Lawan Maiturare a duk aminai na - Bilkisu Yusuf Ali

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!