A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah, ga duk mai yawan rai.
Kamar yau ne aka yi taron murnar sunan Gimbiya Maryamu ‘yar Marubuciya Sa’adatu Baba. Cikin yardar Allah, sai ga shi har ta cika shekaru 13 a duniya.
Hakan ya sa Sa’adatu Baba Ahmad ta shirya wa ‘yar ta wani shagalin biki domin taya ta murnar cika shekaru 13 a duniya.
A cikin wani saƙo da ta wallafa a shafin ta na Facebook, Sa’adatu Baba Ahmad ta yi godiya ga Allah, tare da bayyana farin cikin ta bisa ga cikar ‘yarta Maryamu shekaru 13 a duniya.
Sa’adatu Baba Ahmad dai tana ɗaya daga cikin Marubuta mata da suka daɗe suna bayar da gudummawa a ci gaban Adabin Hausa.
Ta yi littattafai masu yawa, tare da rubuce-rubuce a jaridu da mujallu. Sannan ta na bayar da duk wata gudummawa da take samar da cigaba a harkar rubutu da marubutan Hausa.