A gobe laraba 23 ga Oktoba 2024, za a fara gudanar da taro na wuni biyu domin horas da ‘yan Kannywood kan harkokin kasuwancin fim domin samun dabarun inganta sana’ar su.
Taron wanda za a yi shi ne bisa jagorancin Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, fitaccen kamfanin sadarwa na duniya, Google, ne zai gabatar.
Za a gudanar da taron ne a babban ɗakin taro na Kannywood TV wanda ke kan titin Muhammadu Buhari a cikin garin Kano.
Taron dai zai kasance daga gobe Laraba 23 ga Oktoba zuwa jibi alhamis 24 ga Oktoba 2024, kuma za a fara taron daga ƙarfe 9 na safe a kowacce rana.
Ana sa ran manyan baƙi tare da ‘yan fim daga sassa daban-daban na ƙasar nan ne za su halarci wannan taron.