A GOBE Alhamis ne za a fara bikin Anisa Sa’eed, ɗiyar shahararriyar marubuciyar littattafan Hausa ɗin nan, Hajiya Halima Abdullahi K/Mashi.
Katin gayyatar ɗaurin aure ya nuna cewa za a ɗaura auren Anisa da abin ƙaunar ta, Auwal Abdullahi (A. Prince), a ranar Lahadi, 11 ga Fabrairu, 2024 a Masallacin Mu’azu Abubakar da ke Shagari Close, Unguwar Rimi, Kaduna.
Amma kafin ranar ɗaurin auren, Hajiya Halima za ta yi taron yinin biki a gobe Alhamis, 8 ga Fabrairu, a Mash Event Centre da ke G/Gawa, Maidile a cikin garin Kano da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.

Hajiya Halima dai ita ce Shugabar Ƙungiyar Marubuta Alƙalam da ke Kaduna.
Marubuta da dama sun taya Halima murnar wannan abin farin ciki a soshiyal midiya, tare da yin addu’ar Allah ya ba da zaman lafiya da ƙaruwar arziki.