SAKAMAKON hare-haren ‘yan bindiga da aka yi fama da su a baya-bayan nan, Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal Dare, ya jajanta wa al’ummar da ‘yan bindiga su ka hana zaman lafiya a yankin Zurmi da kewaye.
Gwamnan ya kuma jinjina wa dakarun tsaro saboda ƙoƙarin da su ke yi na kakkaɓe ‘yan bindigar, masu garkuwa da kuma aikata ta’addanci.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan, Malam Sulaiman Bala Idris, ya fitar tare da sa mata hannu, Gwamna Lawal ya bayyana tsananin damuwar sa dangane da hare-haren baya-bayan nan da ‘yan bindiga suka riƙa kaiwa cikin Ƙaramar Hukumar Zurmi.
Ya ce duk da wannan aika-aika da maharan ke yi, rahotanni na nuni da cewa an kakkaɓe manyan kwamandoji da gogarma-gogarman ‘yan bindiga da dama a Zamfara da sauran yankunan Arewa-maso-yamma.
Ya ce: “Gwamnatin Zamfara ta nuna damuwa sosai dangane da hare-haren da ‘yan bindiga su ka kai kwanan nan a yankunan Zurmi, Maru, Tsafe da sauran yankunan jihar.
“Mu na miƙa jaje da ta’aziyya, alhini da damuwa ga dukkan waɗanda wannan farmaki ya shafa, musamman a Ƙaramar Hukumar Zurmi, inda aka rasa rayuka.
“Gwamnatin Jihar Zamfara za ta bayar da tallafin gaggawa da kayan agaji ga waɗanda waɗannan hare-hare su ka shafa. Kuma mu na tabbatar da cewa gwamnati ta maida hankali sosai wajen tabbatar da tsare duniyoyi da rayukan jama’a.
“Mu na kuma sane da irin sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi wajen kare rayukan jama’a. Gwamnatin jiha za ta ƙara taimaka masu da dukkan abubuwan da su ke buƙata wajen yaƙi da ‘yan bindiga.”