GWAMNATIN Tarayya ta haramta haska wani fim ɗin Amurka a gidajen sinima a Nijeriya saboda ya na ɗauke da labarin ‘yan luwaɗi.
Shahararren kamfanin shirya finafinai na masana’antar Hollywood ɗin nan, Marvel Cinematic Universe, shi ne ya shirya fim ɗin mai suna ‘Eternals’, wanda ke ɗauke da labarin gumurzu.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa gidajen sinima a Nijeriya sun tsara cewa za su fara haska fim ɗin a shekaranjiya Juma’a, 5 ga Nuwamba, 2021, to amma sai aka wayi gari aka ga babu sunan fim ɗin a jerin sunayen finafinan da za a nuna a ranar.
Nijeriya ta bi sahun wasu ƙasashen duniya ne da su ka haramta fim ɗin a ƙasashen su.
Hakan ya biyo bayan cacar bankin da ta ɓarke a kan fim ɗin a zaurukan tattaunawa na soshiyal midiya.
Sai dai kuma har yanzu gidajen sinima a Nijeriya ba su bada sanarwa kan dalilin janye fim ɗin daga jerin finafinan da za su nuna ba, sannan ita ma Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (National Film and Video Censors Board, NFVCB) ta yi gum da bakin ta kan lamarin.
Sai dai kuma sanin kowa ne cewa hukumar ba ta sassautawa kan duk wani fim mai nuno wata ɗabi’a da ta danganci soyayya ko tarawa a tsakanin jinsi ɗaya.
Shi dai wannan fim, wata darakta mai suna Chloé Zhao ce ta bada umarni wajen shirya shi, kuma ya tayar da muhawara tun lokacin da labari ya ɓulla game da abin da ya ƙunsa.
A wani labari da mujallar Fim ta samu daga jaridar ‘The Hollywood Reporter’, an bayyana cewa wasu ƙasashen Larabawa da su ka haɗa da Saudi Arebiya, Ƙatar da Kuwait sun haramta nuna fim ɗin saboda nuno ‘yan luwaɗi da aka yi a ciki, musamman bayan sun buƙaci da a cire wuraren da aka nuno soyayya irin ta masu jinsi ɗaya.
Amma wata majiya ta ce ƙasar Dubai za ta nuna fim ɗin a ranar 11 ga Nuwamba kamar yadda aka tsara za a nuna shi a ƙasashen Larabawa a ranar.
A wurin da ake so a cire ɗin, an nuna wasu ‘yan wasa maza su biyu, Brian Tyree Henry da Haaz Sleiman su na sumbantar juna ba ƙaƙƙautawa a matsayin “ma’auratan juna” a wasan.

A wani taro da manema labarai da aka shirya don yayata fim ɗin, jarumar shirin, Angelina Jolie, ta bayyana haramcin da sunan “jahilci”, sannan ta yaba wa kamfanin fim ɗin kan ƙin yarda da ya yi na cire wuraren da aka ce ba a so ɗin.
A wata hira da aka yi da ita, darakta Zhao ta yi fatan ba za a haramta nuna fim ɗin a kowace ƙasa ba saboda ‘yan kallo “su more sosai”.
‘Yan wasan fim ɗin na ‘Eternals’ sun haɗa da shahararrun jaruman nan Angelina Jolie da Salma Hayek da kuma Gemma Chan, Richard Madden, Kumail Nanjiani, Lauren Ridloff, Brian Tyree Henry, Lia McHugh, Don Lee da Kit Harrington.
Waɗanda su ka rubuta labarin su ne Ryan Firpo da Kaz Firpo, yayin da furodusoshin shirin su ne Kevin Feige da Nate Moore.
An kashe dalar Amurka miliyan 200 wajen shirya shi.
‘Eternals’ shi ne fim na farko da kamfanin Marvel ya shirya kan soyayya tsakanin masu jinsi ɗaya.
![]()







