Masu iya magana dai sun ce “Ganimar yaƙi ta mayaƙi ce”. Da alama wannan karin magana ya zo daidai ga wasu daga cikin jaruman fim da suka bayar da tasu gudummawar a wajen yaƙin neman zaɓen Gwamnatin Kano ta Abba Kabir Yusuf, inda a ‘yan kwanakinnan aka raba musu wasu dalla-dallan motoci tare da kuɗin yin lamaba da kuma shan mai.
Wannan rabon motocin da Gwamnatin Kano ta yi a ƙarƙashin Ofishin Babban Mai Taimakawa Gwamna Kan Harkokin Wallafe-wallafe, ‘yan fim da dama da suka taka rawa a tafiyar Kwamkwasiyya sun samu.
Ko da yake, Babban Mai Taimakawa Gwamna Kan Harkokin Wallafe-wallafe, Tajjani Gandu, ya nuna cewar tsarin yanzu aka fara, za a ci gaba da fito da waɗanda suka bayar ga gudummawa a tafiyar domin kyautata musu domin su san ana sane da irin gudummawar da suka bayar a tafiyar.
Cikin waɗanda aka baiwa notocin dai sun haɗa da Alhassan Kwalle, Aina’u Ade, Bashir Nayaya, Dan Magori, Yahanasu Sani, Baba Sogiji, Isiyaku Jalingi, Hassana Musa, da Hussaina Musa.
![]()







