A YAU babu wani mawaƙi irin na zamani da ya ke tashe a kamar Hamisu Sa’id Yusuf, wanda aka fi sani da suna Hamisu Breaker Ɗorayi. Ba wai ba inke, mawaƙin ya sha gaban abokan sana’ar sa ta fuskar yawan masoya.
To amma duk da tashen sa, Hamisu Breaker ya zo da wani salo da ya bambanta shi da sauran mawaƙan da ke cikin masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood, domin kuwa kusan duk mawaƙin da ya yi tashe a cikin harkar za ka ga waƙoƙin fim ne su ka ɗaga shi. Shi kuwa Breaker, sam, ba a cika saka waƙoƙin sa a fim ba. Ko me ya sa hakan? Domin jin yadda abin ya ke, mujallar Fim ta tattauna da shi kwanan nan a Kano, inda ta fara da tambayar shi tarihin rayuwar sa.
Shi kuma fasihin matashin ya ba mu amsa kamar haka: “Suna na Hamisu Sa’id Yusuf, wanda aka fi sani da Hamisu Breaker.
“An haife ni a unguwar Ɗorayi Ƙarama, Unguwar Bello. Na yi firamare a Ɗorayi Ƙarama, sakandare a Ɗorayi Babba.
“Daga nan na dakata, amma ina da burin cigaba da karatu, da yardar Allah.”
Dangane da yadda ya samu kan sa a cikin harkar waƙa kuwa, cewa ya yi: “Tun ina ƙarami na ke da sha’ awar waƙa har na je makarantar Islamiyya. Daga nan dai shi ne asalin samun kai na a cikin harkar waƙa zuwa yanzu.”
Da yake Hamisu ya yi waƙoƙi da yawa, ko wace waƙar ce ya fi so? Amsa: “Waƙar da na fi so ita ce ‘Ke Ce’, waƙar da na ke cewa: ‘A duniya ke ki ka zam farin ciki na, / Idan ba ki nan wa za na bai wa ƙauna?'”
Kamar yadda mu ka ce, duk da cewar Hamisu Breaker a cikin Kannywood ya ke shawagin sa, sai dai ba a cika ganin waƙoƙin sa a cikin finafinai ba. Ko me ya sa?
Amsar sa da ya ba mu ita ce: “Gaskiya ba a cika ji na ba. Dalili na farko shi ne yanayin saƙon da na zo da shi ba irin na fim ba ne, kasancewar yawancin fim waƙa ana sanya maza da mata ne, ni kuma namiji kawai.
“Kuma na lura da yadda za a kawo wani sauyi, kuma Allah ne ke yin komai, kuma ina godiya ga Allah domin ƙwarin gwiwar da na ke da shi bai faɗi a banza ba, domin jama’a sun karɓa kuma da man su ake so su karɓa.

“Wannan ya sa ban raja’a kan waƙoƙin fim ba ko da aka fara ji na, domin mutane sun fi son juna a irin waƙoƙin da na ke yi, kuma za ka ga yawancin su ma ba su da muhalli a fim.”
Da ya ke Hamisu Breaker ya samu ɗaukaka, ya na fuskantar wata matsala a wannan harka kuwa?
“Bayan nasara da ɗaukaka, na ga wasu ƙalubalen da dama,” inji shi. “Shi ma bambancin ra’ayi ne na mutane – wannan ya na son kaza, wancan ya na son kaza. Amma shi ma ɗin kasancewar duk masoya ne, ba sai na bayyana ba. Ba zan so abin da zai shafi masoya na ba.”
Daga ƙarshe, fitaccen mawaƙin ya yi fatan alheri ga ɗimbin masoyan sa da su ke nuna masa ƙauna a kowane lokaci.
![]()







