ANA iya kiran shahararren ɗan kasuwar finafinan Hausa ɗin nan Alhaji Sani Rainbow na ɗaya a harkar kasuwancin finafinan. Akwai lpkacin da babu ɗan kasuwar fim mai fitar da finafinan da su ka kai nasa yawa a kowane wata.
Tuni Alhaji Sani, wanda mazaunin Gusau ne a Jihar Zamfara, ya yi ɓatan dabo daga industiri, an daina ganin finafinan sa a kasuwar gaba ɗaya. Hakan ya faru ne tun daga lokacin da Gwamnatin Tarayya ta ba furodusoshin finafinan Hausa tallafi na miliyoyin kuɗi.
Wasu na ganin kamar Rainbow ya canza sana’a ne, wasu kuma su na cewa ya shiga harkar gwamnatin Jihar Zamfara ne.
Shin ina ya shiga? Mecece gaskiyar cewa ya bar harkar fim? Me ya yi da kuɗin tallafin da gwamnati ta ba shi? Alhaji Sani ya amsa waɗannan tambayoyin da ma wasu a wannan hirar da ya yi da mujallar Fim.
FIM: Sani Rainbow, za mu tattauna da kai game da makomar harkar fim, wadda akwai bambanci tsakanin da da yanzu. A da, a kan ga kusan kowane mako ka kan saki finafinai fiye da biyar a wani lokacin, amma yanzu kuma shiru. A da, idan za ka saki fim kusan duk Nijeriya kowa sai ya san za ka saki. Me ke faruwa ne? Ka aje harkar ne kamar yadda ake yaɗa ji-ta-ji-ta, ka rungumi wata harkar ko ya abin ya ke?
RAINBOW: Alhamdu lillahi, na ji daɗin wannan tambayar da ka yi min. Wato kamar yadda ake yaɗa wannan ji-ta-ji-ta na cewa na bar sana’ar fim, ba gaskiya ba ne. Ni ban daina sana’ar fim ba. Wasu dalilai ne su ka sa mu ka ja da baya, mu ka ɗan yi shiru, saboda mu ɗan ba wasu dama ko kuma waɗanda su ke ganin su ne su ka iya ko kuma su ne za su kawo gyara a cikin harkar. To, shi ne dalilin da mu ka ja da baya. Amma harkar fim, kamar yadda ka sani, ita ta raine mu, cikin ta mu ka tashi, kuma cikin ta mu ke kawo finafinai masu inganci da mutanen duniya su ke yabawa a ciki. Babu yadda za a yi mu bar wannan sana’a ta fim.
FIM: Ana raɗe-raɗin cewa an fi ganin ka cikin harkokin gwamnatin Jihar Zamfara da kuma wasu al’amura na kasuwanci da ake ganin ka na haɓakawa a Zamfara ɗin, wanda ya sa ka yi bankwana da harkar fim. Mecece gaskiyar lamarin?
RAINBOW: E to, kamar yadda na ke gaya maka, wato maganar gaskiyar lamari shi mutum ba a yi shi saboda sana’a ɗaya ba; zai iya bugawa ko’ina da ko’ina ya shiga sana’o’i da yawa da kamfanin shi ko da wasu kamfanoni ya nemi halalin shi.
Sannan kuma alaƙar mu da gwamnati alaƙa ce mai kyau, wanda ya ke mu na da alaƙa da gwamnati, kuma duk inda za mu bada gudunmawa domin gwamnati ta ci gaba za mu iya badawa sosai a ciki.
Sannan kuma ita harkar fim, kamar yadda na ke gaya maka, abin da ya sa mu ka ja da baya, ba wai mu na zargin gwamnatin Jihar Kano ba ne. Gwargwado ita ma gwamnatin Jihar Kano ta bada gudunmawa sosai da sosai a cikin harkar fim. Kuma ita ma mun raɓe ta. Ba ma harkar fim ba kawai, har da wasu harkoki da ya kamata a wayar da kan jama’a da gwamnati duka mu na bada gudunmawa a kai.

Wato ban so na kira suna ba ko kuma na ambaci wani, amma wannan tambayar da ka yi min shi ya sa zan fito in feɗe wa jama’a biri har wutsiya, kuma na gaya masu menene gaskiyar abin da mu ke ciki. Alhamdu lillahi, gwamnatin Kano ta ɗauko ɗaya daga cikin mu, wanda ta ke ganin ta mutunta mu ta karrama mu, ta ba shi wani muƙami a cikin gwamnati, kuma wanda zai kula da wannan sashe na sana’ar finafinai. To, shi kuma da ya zo cikin wannan harkar, ya zo da wani buri a cikin ran shi, sai ya ɗauki hassada da ƙyashi ya kawo shi a ciki. Duk wani wanda aka ce Allah ya ba shi ɗaukaka a cikin sana’ar finafinai, shi ne abin gaba a gare shi, shi ne abin hassada a gare shi, shi ne ya sa a gaba, shi ne ya ke ƙoƙarin sai ya ga bayan shi. To mun ga kamar ya taho ne ya nema ya rusa harkar, ya ci mutuncin mu, ya na so ya yaga mana mutunci ko kuma ya so ya ci zarafin mu gwargwado, ga shi kuma jama’ar gari da waɗanda mu ke mu’amala da su da ita kuma gwamnati ta na kallon mu masu mutunci, masu daraja a idanun ta.
Waɗannan dalilai da su ka sa za a ci mutuncin mu da zarafin mu, mun yi ƙoƙarin lurar da gwamnati haka, ganin kar a ga kamar mun fito mu na yaƙi da shi ne ko kuma mu na adawa da muƙamin da Allah ya ba shi, shi ya sa mu ka ga akwai hanyar sana’o’i da yawa. Wanda ya ke cewa za mu iya saurara wa harkar nan mu je mu yi wasu. Ba mu na fatan babu shi ba, in ya zauna shekara ɗari a kai, yanzu alal misali ba wai mu na alfahari ba ne, daga ni har aboki na Arrahus da irin su darakta Aminu Saira da sauran mutane waɗanda mu ke tafiya tare da su a wannan masana’antar, ai an koka yanzu dalilin rashin mu a masana’antar fim. Ba alfahari ba ne mu ke yi ba. Saboda duk watan Allah sai na kawo fim huɗu kasuwa, ina raba finafinai sama da katan ɗari biyu a cikin wata ɗaya.
FIM: Amma wasu su na ganin kamar matsalar kasuwa na daga cikin abubuwan da su ka tsorata ku, ku ka ja baya.
RAINBOW: Magana ta Allah, fim ɗi na na farko shi ne ‘Garin Mu Da Zafi’, wanda ya ke kasuwar finafinai ta san shi. Na biyu, ‘Jamila Da Jamilu’. Bayan su irin ‘Ƙarangiya’, su ‘Ga Duhu Ga Haske’, da sauran su. Ban taɓa wata ɗaya ba babu wani fim nawa wanda kasuwa za ta neme shi.
To, duk yanayin da ake ciki na kasuwa da rashin daɗin ta da daɗin ta da yanayin kasuwa babu wanda ban cimma ba a cikin harkar finafinan Hausa. Don haka babu wani yanayi na kasuwa da zai tsorata ni a cikin harkar finafinai, saboda ita ce harkar da na fi ƙwarewa a cikin ta fiye da kowace harka.
FIM: To, sai dai kuma a wani ɓangaren akwai kuɗaɗen da ku ka samu na tallafi daga gwamnati domin ku haɗa wannan sana’a, wanda yin haka ‘yan fim da yawa sun yi murna sun yi tsalle, har su na cewa alhamdu lillah, iyayen gidan su sun samu jari ta yadda za a haɓaka harkar, kowa ya samu abin yi, sai kuma ga shi kun yi shiru. Wasu su na tunanin kamar ku na tunanin kun riga kun ci ladar ku, wasu kuma su na tunanin cewa kun canza sana’ar ne gaba ɗaya, da makamantan su. Shin akwai wani albishir wanda idan sauran ‘yan fim su ka ji daga bakin ka za su sa ran cewa lallai da gaske su Sani Rainbow su na nan dawowa a dasa daga inda aka tsaya?
RAINBOW: E. Abin da zan ce maka, waɗannan kuɗaɗen da mu ka samu daga Gwamnatin Tarayya, wanda aka ba mu tallafi a masana’antar finafinan Hausa, ba wai mun raina ba ne. Kuɗi ne masu daraja, kuma mu na godiya da ni da duk kamfanonin da su ka samu. Aƙalla kamfani na na S.A. Rainbow ya samu N24,000,000 (naira miliyan ashirin da huɗu) wanda aka ba ni na tallafi.
Wato abin da na ke so ka sani, wannan N24,000,000 bai kai darajar fim biyu ba wanda na ke kawowa kasuwa. In na buga fim, aƙalla ina kawo fim na N50,000,000 a wata ɗaya a kasuwa. Don haka wannan tallafi da mu ke samu, mu na godiya. Sannan kuma tun tuni wannan tallafin da mu ka samu, irin su ‘Maƙaryaci’, ‘Mafarin Tafiya’, aƙalla fim huɗu kamfani na ya yi da su, kuma waɗannan finafinan su na cikin kasuwa.
Ban ɗauki waɗannan kuɗaɗe na kai su zuwa wata sana’a ba a baya. Wannan dalilin da na faɗa maka na cewa wasu waɗanda su ke ganin sun iya ko kuma su na ganin da wani dama, shi ne dalilin da ya sa mu ka ja da baya.
Amma ina yi wa ‘yan’uwa na masu harkar fim da masu kallon finafinai, furodusoshi ina yi masu albishir da cewa kamfani na na S.A. Rainbow bai daina harkar fim ba, ina nan ciki. Kuma ina yi masu albishir da cewa in Allah ya yarda, in komai ya yi daidai, waɗanda su ke ganin cewa ba mu da wata harka sai wannan harka, ko su na da wata dama, saboda sun samu dama za su kore mu ko za su karya mu, saboda haka mu ka ja baya, su gani ko ba da ita ba ko da ita in Allah ya ce zai raya mu da arzikin mu za mu yi rayuwa, za kuma mu ci gaba da wasu harkokin.
FIM: Zuwa yaushe za a sa ran dawowar ku fagen shirin fim?
RANBOW: In Allah ya yarda nan ba da jimawa ba, ina yi wa mutane albishir, akwai wani sabon kamfani da na ƙirƙiro yanzu haka. Sunan sabon kamfanin ’10 ‘O’7 Entertainment’. Ya yi fim na farko, sunan fim ɗin ‘Mijin Yarinya’, wanda masoyan mu sun gani. Yanzu haka wannan kamfani ya na shirye-shirye zuwa ƙarshen shekarar nan zai yi fim aƙalla za su kai shida. In-sha Allahu zuwa watan Janairu za a gan mu mun dawo cikin wannan sana’ar.
FIM: A matsayin ku na manya a harkar fim, akwai wani shiri na musamman da ku ke yi na gyara wa industiri zama, musamman ɓangaren yaƙi da masu satar fasaha, wanda ku ka fi yawan kuka da cewar su ne su ka dabaibaye harkar, har ta kai ga wasu masu jarin sun karye, wasu kuma ga su nan dai ba su mutu ba, ba kuma su yi rai ba?
RAINBOW: Wato ni abin da na ke so in faɗa maka, ba wai in mun dawo ba. Har yanzu ina da finafinai aƙalla za su kai goma, waɗanda su ke hannu ban sake su ba. Ka ga ko duk wanda ya ke da finafinai goma babu inda ya tafi. Wannan ɗan hutun da mu ke yi na sanar da kai dalilin da ya sa mu ke yi. Mu na nan dawowa. Kuma sannan wannan yaƙi da mu ke yi da masu satar fasaha da kuma masu sauke finafinan mu su na tura wa mutane ta waya, dama da ni da aboki na Arrahus mu na ƙoƙarin yaƙi da waɗannan harkokin na masu satar fasaha. Kasancewar yanzu da mu ka ɗan ja baya, shi ya sa wannan farisin ka ga ya dawo ya yi girma sosai. Allah ya saka wa Arrahus da alheri, ya saba ya fitar da kuɗi a cikin dukiyar sa ya wakilta mutane a kowace jiha a kamo masu yi mana satar fasaha da masu ‘downloading’, a zo a gurfanar da su gaban kotu. A lokacin da aka yi barazarar a kama shi a gurfanar da shi a gaban kotu ba tare da ya aikata wani laifi ba, saboda wani cin zali na daban. Wannan ya na ɗaya daga cikin abin da ya sa ya ja baya. Tun da ya ja baya, babu wani wanda ya ke iya fitowa ya yaƙi ‘yan faresi ɗin nan. Ita kuma gwamnati in dai ga mai aikata laifi, sai ka rubuta ƙorafi sannan za a ba ka dama, ku zo a fita a je a yi, tunda faresi ɗin ba iyakar hurumin Jihar Kano ba ne, duk jihohi ana yin shi. Gwamnatin Tarayya kuma ta ba mu goyon baya da ‘yan sanda duk mu na zuwa mu na kama masu satar fasaha ɗin nan. To, waɗanda aka bari a cikin harkar, ana ganin su ne ‘yan lele, su ne ‘yan kan gaba, ba su iya fita su je su yi wannan aikin. Ka ga ko nan an ga amfanin mu, in mu ka dawo kuma a shirye mu ke da mu yi yaƙi da faresi. Kuma ko yanzu da ba mu a cikin harkar mu na bada gudunmawa na hanawa da komai. Kuma ko yanzu a shirye mu ke yi mu yi maganin masu wannan gurɓatattar sana’ar mataki.
FIM: Wani abu kuma shi ne wasu na ganin rashin ingantacce ko kuma tsayayyen shugabanci a industiri ya bada gudunmawa wajen haifar da matsaloli makamantan waɗannan. Kai me za ka ce?
RAINBOW: Alhamdu lillahi, ni abin da na ke magana, ba a cewa rashin tsayayyen shugabanci. Saboda akwai ƙungiyoyi da dama a cikin wannan masana’antar. Kuma duk waɗannan ƙungiyoyi shugabannin su zaɓen su ake yi. Ka ga ko ba a cewa babu tsayayyen shugabanci. Sai dai abin da za a ce, rashin tsawatarwa da kuma bin doka da oda na kundin tsarin ƙungiyoyin. To, shi ya sa ba a iya tsawatarwa, kowa ya na fitowa ya na ganin shi babba ne, ya na abin da ya ga dama.
Ka ga ya na da kyau a ce a samu ƙungiya guda ɗaya ta ja gaba tare da sauran ƙungiyoyin ‘yan wasa, furodusoshi, ‘yan kasuwa da sauran su. Wanda idan ta sa doka kuma kowa zai bi ta, duk wanda ya taka dokar kuma za a hukunta shi. Amma rashin bin dokar ya na farowa ne da shugaban. Za ka ga shugaba shi zai fara taka doka. Ka ga ko in ya taka doka, na ƙasa da shi ba za a shi dole ya bi doka ba.

FIM: Me za ka ce dangane da yadda gidajen talbijin su ke gasar karɓar finafinan ku su na nunawa a talbijin? Hakan za a iya ɗaukar shi a matsayin kishiya ga kasuwar finafinai ko kuma ka na ganin haka ya fi yi wa ‘yan fim riba? Kuma ka na ganin ba zai kawo cikas a ɓangaren kasuwa ba?
RAINBOW: Wannan cigaba ne. Wato alakulli halin za ka ga duk fim ɗin da ka ga an kai gidan talbijin, sai bayan mun gama cin shi a kasuwa kamar yadda aka saba. Lokacin ya na kasuwa za a samu gidan talbijin kamar guda goma, wannan ya saya, wannan ya saya, domin shi ma ya haska. Wato kamar mu yanzu finafinan namu ba mu iya isar da su ga duk wani wanda ya ke buƙatar kallon su a faɗin Nijeriya, balle kuma maƙwabtan ta. Ka ga inda mu ka tsaya su kuma gidan talbijin za su haska ya kai inda bai kai ba, kusan duk duniya za a gani. Ka ga wannan ai ba cibaya ba ne, cigaba ne. Sannan su gidan talbijin ɗin su na samu, haka su ma furodusoshin mu da ‘yan kasuwa su na samu. Don haka wannan ba zai taɓa kasuwar mu ba, sai dai ya ƙara haɓaka harkar kasuwanci.
FIM: A ƙarshe, ka na da wani jan hankali ga takwarorin ka ‘yan fim da kuma masoyan ka?
RAINBOW: Alhamdu lillahi! Jan hankalin da zan yi wa takwarori na ‘yan fim, a ko da yaushe a riƙe gaskiya da riƙon amana. Mu daina shirya finafinai waɗanda ba su dace da addini da al’ada ba. Sannan duk wani wanda su ka gani Allah ya ba shi dama a riƙa girmama shi, a daina sa hassada ko ƙyashi a gaba ko kuma ana ganin wani ya zama wani abu ko kuma ana ganin shi baƙo ne, yaushe ya shigo harkar ko kuma ba ma ainihin ɗan jihar da ake shirya finafinan ba ne. Ni shawarar da zan ba su kenan. Su kuma masoyan mu, ina yi masu albishir da za mu dawo mu ci gaba da kawo masu ingantattun finafinai.
FIM: Mun gode, Sani Rainbow.
RAINBOW: Ni ma na gode, mujallar Fim.