TSOHUWAR jaruma Wasila Isma’il ta yi murnar zagayowar ranar haihuwar ta a yau.
Wasila, wadda ita ce matar fitaccen jarumi kuma darakta Al-Amin Ciroma, ta bayyana murnar ta ne ta hanyar wallafa wasu hotuna nata guda goma a Instagram da kuma wani bidiyo da aka yi da harhaɗa hotunan, aka kuma sanya waƙar fim ɗin ‘Wasila’ daga baya.
Sai dai jarumar mai ritaya ba ta faɗi ko shekaru nawa ta cika a duniya ba.
Ɗimbin mutane sun taya Wasila murna tare da yi mata addu’ar fatan alheri.

Shi ma mijin ta, wanda shi ne shugaban gidan talbijin na Farin Wata da ke Abuja, ya wallafa hoton ta tare da taya ta murna.
Idan kun tuna, kwana huɗu da su ka gabata, a ranar 6 ga Oktoba, 2021, Wasila da Al-Amin su ka yi murnar cikar auren su shekaru 19.
Allah ya albarkaci rayuwa, amin.
Ga hotunan da Wasila, uwar ‘ya’ya huɗu, ta wallafa a yau.







