FITACCEN mawaƙi kuma jarumi, Adamu Hassan Nagudu, a yau ya saki sababbin hotunan da ya ɗauka tare da iyalin sa a Instagram, tare da yin addu’ar fatan alheri.
A hotunan guda bakwai, an ga Adamu tare da maiɗakin sa da kuma ‘ya’yan su biyu, duk maza.
Ya na sanye da manyan kaya masu ruwan goro, irin kalar zani da riga da matar sa ta sa, yayin da ‘ya’yan su ke sanye da ƙananan kaya.
Akwai alamar farin ciki da annashuwa a fuskokin su su duka.


A yayin da sun yi hotuna biyar na farko a cikin falo, sauran biyun kuma sun yi su ne a waje, ɗaya ma Adamun ne da ɗan sa a cikin motar sa.
A ƙasan hotunan, Adamu Nagudu ya yi addu’ar fatan alheri, inda ya ce: “Alhamdu lillah. Allah ka ƙara mana zaman lafiya da yalwar arziki da tsawon kwana mai amfani, ka zaunar da ƙasar mu Nijeriya lafiya, idan mutuwa ta zo ka sa mu cika da imani, abin da mu ka bari baya ‘ya’ya da iyayen mu Allah kai riƙo da hannayen su alfarmar Annabi Muhammadu s.a.w.”


To, Adamu, mu ma a mujallar Fim mun ce amin, kuma Allah ya ƙaro maku ƙauna da arziki.
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com