WAƊANNAN wasu ne daga hotunan taron gangamin da ‘yan fim su ka yi don yi wa babbar furodusa marigayiya Hajiya Umma Ali addu’a.
An yi taron a Social Welfare da ke Gyaɗi-Gyaɗi, Kano.

Hajiya Umma ta rasu a rana i ta yau, Lahadi, sakamakon rashin lafiya. Shekarun ta 63.

An gudanar da taron a ƙarƙashin Majalisar Dattawan Kannywood, wato Kannywood Foundation.
Allah ya jiƙan Hajiya Umma Ali, amin.





