HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta ba da umarnin rufe dukkan gidajen gala da ke faɗin jihar.
Umarnin ya biyo bayan ƙaratowar azumin watan Ramadan.
Sanarwar rufe gidajen, wanda jami’in yaɗa labarai na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a yau, ta ce, “Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ab’i ta Jihar Kano, Alh. Abba El-Mustapha, ya ba da umarnin rufe dukkannin gidajen gala da sauran guraren wasanni a Jihar Kano har zuwa kammala ibadar ta azumin.”
Da yake jawabi a yayin kafa wani kwamiti na kar ta kwana ƙarƙashin Mal. Nasiru (Shehi), El-Mustapha ya ce, “Aikin wannan kwamitin shi ne ya tabbatar da babu wani gidan wasa a Jihar Kano da suke gudanar da wasa a lokacin azumi.”
Haka kuma ya sha alwashin yin hukunci mai tsauri ga duk mai gidan wasan da aka samu gidan sa da karya wannan doka.
Haka kuma wannan umarnin ya haɗa hana dukkan ‘yan wasa zama a gidajen wasan su har tsawon wannan lokaci na azumi.
A ƙarshe ya yi kira ga ƙungiyar masu gidajen wasannin da su saka ido sosai ga ‘ya’yan ƙungiyar su domin tabbatar da sun yi biyayya ga wannnan sabon umarni.
El-Mustapha ya kuma gode wa malamai tare da al’ummar jihar dangane da shawarar da suke ba shi tare da nuna goyon bayan su a gare shi tsawon lokaci tun fara aikin sa a matsayin sabon Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.
![]()







