• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Hukumar Tace Finafinai na samun cigaba a ƙarƙashin El-Mustapha, inji Sarkin Kano

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 16, 2023
in Labarai
0
Sarkin Kano tare da Abba El-Mustapha a lokacin ziyarar

Sarkin Kano tare da Abba El-Mustapha a lokacin ziyarar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAI Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta na samun cigaba a ƙarƙashin sabon Babban Sakataren ta, Alhaji Abba El-Mustapha.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya ce sarkin ya faɗi haka ne a lokacin da shugaban hukumar ya jagoranci tawaga daga hukumar sa su ka kai wa sarkin ziyarar ban-girma a fadar sa a jiya Laraba.

Ya ce a lokacin ziyarar, sarki ya yaba wa cigaban da aka samu a hukumar a ƙarƙashin shugabancin El-Mustapha, wanda sarkin ya bayyana shi a matsayin haziƙi kuma jajirtacce, mai son kawo wa al’ummar Jihar Kano cigaba.

Haka kuma sarkin ya gode wa Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf dangane da dogon nazari da ya yi lokacin da ya zaɓo El-Mustapha a matsayin sabon shugaban hukumar. 

Mai Martaba Sarki tare da tawagar maziyartan daga Hukumar Tace Finafinai

Ya kuma bayyana ƙarfin gwiwar sa tare da cewa tun lokacin da aka ayyana sunan Abban a matsayin wanda zai jagoranci hukumar al’ummar sa da dama ke nuna gamsuwar su da cewa lallai an ɗora ƙwarya a gurbin ta.

Sarkin ya ba hukumar tabbacin cewa ƙofar su za ta ci gaba da zama a buɗe a ko da yaushe domin shawara ko gudunmawa.

A nasa ɓangaren, El-Mustapha ya bayyana wa sarki cewa ya kai masa ziyara ne domin girmamawa tare da neman albarka ta yadda zai cimma nasarar da hukumar ta sa a gaba.

Ya kuma yi wa sarkin addu’ar Allah ya ja zamanin sa, ya ƙara masa nisan kwana.

El-Mustapha da tawagar sa a fadar Kano

Loading

Previous Post

Aiki sai mai shi: Ayyukan raya jiha da inganta rayuwar jama’a fiye da 300 a Kasafin 2024 na gwamnatin Namadi a Jigawa

Next Post

Editan finafinai a Kannywood, Hafiz SB zai yi bankwana da kwanan shago

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Hafiz Hamisu da katin gayyatar auren sa

Editan finafinai a Kannywood, Hafiz SB zai yi bankwana da kwanan shago

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!