HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta ƙwace aikin yin rajistar ‘yan fim daga hannun ƙungiyoyin ‘yan fim da ta damƙa masu a baya zuwa ofishin ta da ke Titin Maiduguri a cikin garin Kano
Haka kuma ta bayar da tsawon mako uku ga duk wanda bai yi rajistar ba, to ya zama wajibi ya je ofishin ta ya yi rajista domin kauce wa ɗaukar matakin da ya dace a kan sa.
Bugu da ƙari, hukumar ta bayar da umarnin hana ɗaukar duk wani fim ko sakin sa ba tare da an tace shi ba, ta ce saɓa wannan umarnin ka iya saka mutum ya fuskanci fushin doka tare da yin da na sani.
Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, shi ne ya ba da sanarwar hakan a jiya Litinin a cikin jawabin sa ga manema labarai tare da jagororin ‘yan masana’antar Kannywood da su ka haɗa da Kannywood Foundation, Arewa Film Markers, Artists Guild of Nigeria (AGN), da kuma MOPPAN.
El-Mustapha ya jaddada cewa hukumar ta bai wa ‘yan masana’antar kannywood wa’adin sati Uku, wato daga ranar 10 ga Yuni zuwa 1 ga Yuni, 2024, don kowa ya zo ya yi rajista kafin ‘yan kwamitin su fara aiki.
‘Yan kwamitin da za su yi aikin sun haɗa da wakilan ƙungiyoyin da aka yi wannan zaman da su da kuma ma’aikatan hukumar.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa da ma can dokar da ta kafa hukumar ta ba ta ikon yi wa ‘yan fim rajista.
Tun a farkon zuwan sa hukumar, El-Mustapha a ƙoƙarin sa na kawo gyara tare da tsaftace harkar fim, ya kawo sababbin tsare-tsare, ciki har da sabunta rajista ga dukkan masu gudanar da sana’a a Kannywood. Hakan ya jawo surutai tare da tayar da ƙayar baya ga wasu daga cikin ‘yan fim, musamman ma waɗanda su ke cikin gwamnatin, irin su darakta Sunusi Oscar 442 wanda shi ne Babban mai ba Gwamanan Kano shawara a kan harkar fim.
Bayan kai ruwa rana ne da aka samu a wancan lokacin bisa neman maslaha, hukumar ta dawo da yin rajistar ‘yan fim ɗin zuwa hannun ƙungiyoyin ‘yan fim ɗin kamar yadda su ka buƙata.
Sai dai tun daga lokacin da tsarin rajistar ya dawo hannun kungiyoyin babu wani abu da aka samu na ci gaba da yin rajistar.
Wani bincike da mujallar Fim ta gudanar a tsakanin ‘yan fim ɗin ya tabbatar da cewar tun da aka fara yin rajistar zuwa yanzu ‘yan fim kashi biyu cikin ɗari ne su ka yi rajista, sun haɗa har da mutane 50 da babban furodusa Abdul Amart Mohammed ya biya wa kuɗin rajistar.
![]()







