SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, a yau Laraba ya ƙaddamar da fara ba da takardar shiga gasar ƙirƙirarrun labari ga waɗanda su ke da sha’awa.
Gasar da ita ce ta farko da hukumar ta fara sakawa tun bayan kafa ta a shekarar 2001.
A wata sanarwa ga manema labarai da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya rattaba wa hannu, wadda aka turo wa mujallar Fim, hukumar ta ce: “Manufar gasar shi ce farfaɗo da ɓangaren rubuce-rubuce tare da ƙara wa marubutan Hausa ƙarfin gwiwa, sa wa matasa sha’awar karance-karancen adabin Hausa da kuma kasancewa a matsayin wata hanya da matasa za su dogara da kan su.”
Ta ƙara da cewa kowa na da damar shiga gasar, ba ‘yan Jihar Kano kaɗai ba.
Domin samun ƙarin bayani za a iya kiran wannan lambar wayar: 07060757619
El-mustapha na yi wa kowa fatan nasara da addu’ar Allah ya ba mai rabo sa’a.
![]()







