HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta saka gasa ga marubutan jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne wanda ya ba da sanarwar gasar a cikin wata takarda ga manema labarai da ya saki a yau Asabar, 1 ga Yuni.
Malam Abdullahi ya ce, “Ina marubutan Kano masu sha’awar nuna bajintar su? Ga dama ta samu.”
Ya ci gaba da cewa, “A ƙoƙarin ta na ƙarfafa gwiwa ga marubuta tare da farfaɗo da rubutun ƙirƙirarrun labarai da karanta su a tsakankanin matasa a Jihar Kano, Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya umarci daraktan sashin da ke lura da ɗab’i na hukumar, ƙarƙashin jagorancin Abubakar Zakari G/Babba, da ya sanar da marubuta masu sha’awar nuna baiwar da Allah ya yi musu ta rubutu, hukumar ta shirya gasa a tsakankanin su karo na farko 2023/2024. Ga duk mai sha’awar gasar zai duba ƙasan wannan sanarwar domin cika ƙa’idar da aka saka.
- Ga duk mai sha’awar shiga wannan gasa zai ziyarci ofishin hukumar mai hawa na uku a gidan talabijin ɗin Abubakar Rimi da ke kan Titin Maiduguri, Hotoro, Kano, yayin da zai karɓi shaidar shiga gasar tare da maido ta ga hukumar bayan an cike, daga 5/6/2024 zuwa 19/6/2024.
- Ga duk mai sha’awar shiga gasar ya na da kyau ya sani cewa sati biyu ya ke/ta ke da shi kacal domin kawo rubutun da aka yi domin tantancewa.
- Haka kuma, waɗanda su ka shiga gasar za su iya zuwa hukumar kai-tsaye su ba da rubutun su ko aiko da shi zuwa ga wannan adireshi:
babangidamuhammadbala36@gmail.com.
Domin neman ƙarin bayani za a iya tuntuɓar waɗannan lambobin waya kamar haka: 08036903399 ko 07060757619.
A ƙarshe, hukumar ta yi wa kowa fatan fara wannan gasa a cikin nasara tare da ƙarfafa gwiwar ba da gwaggwaɓar kyauta ga waɗanda su ka yi nasara a gasar.
![]()







