HUKUMAR Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta sha alwashin taimaka wa Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba El-mustapha a duk lokacin aka buƙace ta domin cimma nasarar ayyukan da hukumar ta sa a gaba.
Daraktan hukumar ta DSS, reshen Jihar Kano, Alhaji Hassan I. Muhammad, shi ne ya faɗi haka a yayin wata ziyarar ƙarfafa alaƙar aiki da Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya kai masa ofishin sa a yau Litinin.
Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Tace Finafinan, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya faɗi yadda ziyarar ta gudana a cikin wata sanarwa, ya ce: “Alhaji Hassan I. Muhammad ya ba da tabbacin yin aiki tare da Hukumar Tace Finafinan a kowane lokaci ba tare da samun wata tangarɗa ba.”
Ya kuma ƙara yin alƙawarin barin ƙofar sa a buɗe domin ba da shawara ko wani agaji na gaggawa ga hukumar.

A nasa jawabin, El-Mustapha ya nuna farin cikin sa tare da gamsuwa da irin yadda shugaban DSS ɗin ya tarbi jami’an hukumar tace finafinai a ofishin su.
Haka kuma ya yi godiya ta musamman tare da nuna ƙarfin gwiwa dangane da alƙawuran da hukumar ta DSS ta yi wa hukumar sa na ba ta agajin gaggawa tare da yin aiki tare ta yadda ba za a samu wata matsala ba.
A ƙarshe ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da taimakon daraktan tare da ba DSS ƙarfin gwiwar yin aiki domin sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.