• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 22, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta gargaɗi sababbin kwamishinonin zaɓe da su nisanci ‘yan siyasa ko shiga gidan gwamnati

by DAGA WAKILIN MU
November 4, 2022
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban INEC, ya na gabatar da jawabi ga sababbin kwamishinonin zaɓen da ya rantsar

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban INEC, ya na gabatar da jawabi ga sababbin kwamishinonin zaɓen da ya rantsar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargaɗi sababbin kwamishinonin zaɓe da ya rantsar da cewa su nisanci shiga harkokin siyasa ko yin tarayya da ‘yan siyasa, sai fa a bisa ƙa’idar da doka ta tanadar.

Yakubu ya buƙace su da su tabbatar su na bin dukkan tsare-tsaren da dokar zaɓe ko dokar ƙasa ta shimfiɗa wajen gudanar da aikin su.

Shugaban ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da ya ke rantsar da sababbin Kwamishinonin Zaɓe 19.

Ya ce ya zama tilas su kasance su na aiwatar da komai a bisa ƙa’ida, ba tare da nuƙu-nuƙu ko fifita wani ɓangare ba.

Yakubu ya ce: “Kuma a duk lokacin da ku ke ganawa da masu ruwa da tsaki, to ku kasance ba ku wuce ƙa’idar da dokar ƙasa ta gindaya maku.

“Haka ma a yayin tuntuɓar juna tsakanin ku da jama’a, kada ku tsallake iyakokin da dokar ƙasa ta hana ku tsallakawa.

Kwamishinonin Zaɓen su na ɗaukar rantsuwa a gaban shugaban INEC

“Sannan ku nisanci kai ziyara ofishin gwamna. Wato ba a son a gan ku gidan gwamnati. Kuma kada su riƙa keɓewa ku na ganawa da ‘yan siyasa ba bisa ƙa’idar aikin ofis ba. Ko bayan tashi daga ofis, ba a yarda su riƙa keɓancewa da ‘yan siyasa ba.

“Ku tuna gwamnatin tarayya ku ke wa aiki, saboda haka ita ce abin biyayya a gare ku. Don haka kada ku kauce daga turba, gudun kada ku kai ga zubar da ƙimar ku da darajar INEC.

“Kuma ina ƙara jaddada maku cewa hanyar amfani da tsarin tantance sahihiyar rajistar zaɓe ta BVAS ce kaɗai hanyar da aka amince a tantance mai rajistar zaɓe.”

Daga cikin sababbin kwamishinonin da Yakubu ya rantsar akwai Uzochukwu Chijoke a Jihar Abiya, Nuru Inusa a Adamawa, Elizabeth Agu a Anambara, Mahmood Nura a Bauchi, Samuel Egu a Binuwai, Yomere Otitsemolebi a Kuros Riba da Onyeka Ugochi a Ebonyi.

Loading

Tags: BVASDokar ZaɓeHukumar ZaɓeINECkwamishinonin zaɓemahmood yakuburajistar zaɓesiyasa
Previous Post

Aure: Isma’il Afakallah da Ruƙayya Dawayya sun zama ɗaya

Next Post

‘Rule No. 1’ ya lashe gasar Bikin Baje-kolin Finafinai na Duniya na Abuja

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Zakarun gasar Bikin Baje-kolin Finafinai na Duniya na Abuja

'Rule No. 1' ya lashe gasar Bikin Baje-kolin Finafinai na Duniya na Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!