• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, July 21, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta gayyaci ‘yan takarar shugaban ƙasa zuwa taron sa-hannun amincewa a gudanar da zaɓe cikin lumana

by DAGA WAKILIN MU
February 19, 2023
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu ya na duba babban zauren Cibiyar Taro ta Duniya (ICC)

Farfesa Mahmood Yakubu ya na duba babban zauren Cibiyar Taro ta Duniya (ICC)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa za su bayyana a ranar Laraba, domin su sa hannu kan yarjejeniyar amincewar yarda a gudanar da zaɓe lami lafiya, ba tare da tashin hankali ba.

Yakubu ya bayyana haka a lokacin ganawar sa da ‘yan jarida, bayan ya kai ziyara Makarantar Sakandire ta Garki, Abuja, inda ake bayar da horo ga Masu Sa-ido Kan Jami’an Zaɓe (SPO).

Shugaban na INEC ya kuma kai irin wannan ziyarar a Cibiyar Taro ta Duniya (ICC), inda ya ce a can ne jihohi za su riƙa aikawa da sakamakon zaɓe ana tattarawa. Daga ƙarshe kuma a can ne shugaban na INEC zai bayyana ɗan takarar da ya yi nasara, tare da sakamakon da kowane ɗan takara ya samu.

Yakubu ya ce haka kuma ICC za ta kasance Cibiyar Yaɗa Labarai.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, tare da Mataimakiyar Sakataren Harkokin Ƙasashen Ketare ta Amurka mai kula da Al’amuran Afrika, Molly Phee, da Jakadiyar Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard, lokacin ziyarar su a hedikwatar INEC don tattauna batun zaɓen 2023

Haka kuma Yakubu ya ce INEC ba za ta fuskanci matsalar ƙarancin kuɗi ba, bisa dogaro da alƙawarin da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya yi wa shugaban na INEC, a lokacin da ya ziyarce shi.

Ya ce yawancin ayyukan da INEC za ta biya ma’aikata duk tura masu a asusun ajiyar su za ta yi.

Da ya ke magana kan ƙalubalen tsaro, ya ce wannan aikin jami’an tsaron ƙasa ne, kuma sun yi alkawarin babu wani gagararren da za’a bari ya haifar wa zaɓen 2023 da cikas.

Ya ce Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na Ƙasa da ke ƙarƙashin tsohon  Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar (ritaya), shi ne zai shirya taron rattaba hannun amincewar da ‘yan takarar za su yi a ranar Laraba, 22 ga Fabrairu, 2023, a ICC a Abuja.

Ya ce INEC ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen 2023 a cikin kwanciyar hankali.

Loading

Tags: 'yan jaridaBVASCBNICCINECmahmood yakubuUS Embassy AbujaZaɓen 2023
Previous Post

Maishadda ya yi raddi ga masu tsegumi kan ziyarar gidan Halima Atete da su ka yi

Next Post

Matasan NYSC kaɗai INEC ta amince su yi aiki da na’urar tantance masu katin rajista – Yakubu

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Farfesa Mahmood Yakubu ya na jawabi lokacin da shugabannin INEC su ka kai ziyara a cibiyar horas da jami'an zaɓe a GSS Garki, Abuja

Matasan NYSC kaɗai INEC ta amince su yi aiki da na'urar tantance masu katin rajista - Yakubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!