• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Maishadda ya yi raddi ga masu tsegumi kan ziyarar gidan Halima Atete da su ka yi

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
February 19, 2023
in Labarai
0
Amarya Halima Yusuf Atete tare da maziyartan ta daga Kannywood

Amarya Halima Yusuf Atete tare da maziyartan ta daga Kannywood

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAN furodusan nan Abubakar Bashir Maishadda ya yi martani kan ƙurar da ziyarar da shi da wasu ‘yan Kannywood su ka kai wa tsohuwar jaruma Halima Atete a gidan mijin ta a Maiduguri, Jihar Borno.

Maziyartan, waɗanda su ka dira a gidan a ranar Juma’a da ta gabata, sun haɗa da  Bashir Abubakar Maishadda, Yakubu Muhammad, Garzali Miko da Ibrahim Sharukan.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa tun bayan bayyanar hotunan ziyarar jama’a da dama su ke tofa albarkacin bakin su, musamman a soshiyal midiya. Yayin da wasu ke ganin abin burgewa ne, wasu kuma na ganin sam ba su kyauta ba, wai wannan wani salo ne na hana ta zaman gidan miji ko kuma su sa hankalin ta ya dawo kan harkar fim har ta juya wa mijin ta baya.

Ganin yadda maganar ta ke ci gaba da yamutsa hazo ne ya sa mujallar Fim ta nemi jin ta bakin ɗaya daga cikin ‘yan fim ɗin da su ka kai ziyarar, wato Maishadda, don jin abin da zai ce game da surutan da ake yi.

Daga hagu: Garzali Miko, Abubakar Bashir Maishadda, Halima Atete da Yakubu Muhammad

Furodusan ya ce: “Rabu da mutane kawai a kan maganar da su ke faɗa! Mu dai da kyakkyawar manufa mu ka yi.”

Maishadda ya ƙara da cewa, “Ba wai takanas mun je gidan Halima Atete ba ne, a’a, wani uzirin mu ne ya kai mu garin, kuma sai mu ka je gidan ta a matsayin ta na ‘yar’uwar mu, mu ka ziyarce ta a gidan ta. Don haka mu abu ne mu ka yi da kyakkyawar manufa. 

“Masu magana kuma su je su yi ta yi, mu dai ziyarar sada zumunci mu ka je yi ba don mu kashe mata aure ba.”

Maishadda da Halima Atete a falon ta a Maiduguri

Loading

Tags: Abubakar Bashir MaishaddaGarzali MikoHalima Yusuf AteteIbrahim SharukhanMaidugurimartaniYakubu Muhammadziyara
Previous Post

Kotu ta sake tura Murja Kunya da wasu mutum uku zuwa kurkuku

Next Post

INEC ta gayyaci ‘yan takarar shugaban ƙasa zuwa taron sa-hannun amincewa a gudanar da zaɓe cikin lumana

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Farfesa Mahmood Yakubu ya na duba babban zauren Cibiyar Taro ta Duniya (ICC)

INEC ta gayyaci 'yan takarar shugaban ƙasa zuwa taron sa-hannun amincewa a gudanar da zaɓe cikin lumana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!