Sannu dai ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba domin kuwa tsawon lokaci da aka shafe ba a ganin Jaruma kuma Furodusa a cikin harkar fim, Sapna Aliyu Maru, ashe dai ta koma makaranta ne ta ci gaba da karatun ta na digiri a Jami’ar Skyline, har ta kai ga kammalawa.
Domin kuwa a bikin yaye ɗalibai da Jami’ar Skyline ta yi a ranar Lahadi, 17 ga Nuwamba, Jaruma Sapna tana ɗaya daga cikin ɗaliban da suka kammala karatun digiri a jami’ar na wannan shekarar.
Daman dai Sapna Aliyu Maru ba iya harkar fim din kaɗai ta tsaya ba, domin tana ɗaya daga cikin jarumai mata da suka yi fice a harkar kasuwanci.
Kuma gashi a yanzu ta shiga cikin mata masu kwalin shaidar digiri a cikin Kannywood.
Muna yi mata fatan alheri da kuma samun nasara a mataki na gaba.