ALLAH Akbar! Rai baƙin duniya. Allah ya ɗauki ran jarumi kuma furodusa a Kannywood, Sulaiman Gambo, wanda aka fi sani da Sulaiman Alaƙa.
Sulaiman ya rasu da rana a yau Litinin, bayan ya yi fama da gajerar rashin lafiya.
Za a yi jana’izar sa da misalin ƙarfe 4:00, bayan sallar La’asar, a gidan su da ke unguwar Gwammaja, Kano.
Allah ya jiƙan sa, ya kuma albarkacin dukkan abin da ya bari.