INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura) rasuwa a cikin daren nan.
Ya rasu a asibiti a Kano bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Babu wani cikakken bayani a kan rasuwar a yanzu, amma idan kun tuna mujallar Fim ta ba ku labarin rashin lafiyar sa a makon jiya, inda mu ka yi hirar ƙarshe da shi.
A labarin da mujallar ta buga a ranar 20 ga Satumba mai taken “Umar Bankaura Ya Buƙaci Addu’ar Jama’a Saboda Matsanancin Rashin Lafiya Da Ya Ke Fama Da Shi,” mun ruwaito cewa ɗan wasan kwaikwayon ya bayyana buƙatar addu’a daga al’ummar Annabi saboda yanayin rashin lafiyar da ya ke ciki, wanda ya kai har an kwantar da shi tsawon lokaci a wani asibiti a Kano.
Ga labarin kamar haka:
“Bankaura, wanda a yanzu ake kira Yakubu Ka-Fi-Gwamna saboda rol ɗin sa a diramar ‘Kwana Casa’in’ ta gidan talbijin na Arewa 24, ya na daga cikin daɗaɗɗun ‘yan wasan kwaikwayo da Arewa ke ji da su, domin ya fara dirama ne tun kafin a assasa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.
“Lokacin da wakilin mujallar Fim ya samu labarin rashin lafiyar, ya garzaya gidan sa da ke unguwar Hotoro Tsamiyar Boka a ranar Litinin, 19 ga Satumba, 2022.”
Daga can aka tura shi wani asibitin kuɗi mai suna Pinnacle Special Hospital da ke unguwar Hausawa kusa da Masallacin Murtala inda ya same shi a kwance magashiyan.
“Wakilin mu ya ruwaito cewa da ƙyar ya gane ɗan wasan saboda yadda rashin lafiyar ya ci ƙarfin sa, ya zama kamar ba shi ba.
“Daga kwance a gadon sa na jinya, Bankaura ya faɗa wa wannan mujallar cewa: ‘Ka zo lokacin da ba zan samu damar da zan iya doguwar magana da kai ba saboda yadda na ke a yanzu, amma na gode da zuwan ka waje na.’
“Duk da haka, ya ɗan yi bayanin cewa: ‘Na samu lokaci mai tsawo ba ni da lafiya, domin tun a watan Ƙaramar Sallah na ke cikin rashin lafiyar.
‘”Kuma dai ka ga a yadda ka same ni. Kuma ina fatan ku ci gaba da yi mani addu’a; Allah shi ya san yadda zai yi da bayin sa.’
“Haƙiƙa duk wanda ya san Bankaura, idan ya gan shi sai ya tausaya masa, domin ya na cikin yanayi na buƙatar taimako.”
A ƙarshen labarin, mujallar Fim ta yi addu’ar Allah ya ba shi lafiya, ya sa cutar ta zama kaffara a gare shi.
Allahu Akbar! Ashe ciwon ba na tashi ba ne.
Allah ya rahamshe shi, ya sa ƙarshen wahalar kenan, amin.