• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 5, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kannywood: El-Mustapha ungulu da kan zabo ne, inji Sunusi Oscar

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 22, 2023
in Labarai
0
Sunusi Oscar 442 (a hagu) da Abba El-Mustapha

Sunusi Oscar 442 (a hagu) da Abba El-Mustapha

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAN Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano kan Masana’antar Kannywood, Malam Sunusi Hafiz (Oscar 442), ya bayyana cewa sabon Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i na Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, “ungulu da kan zabo” ne kuma naɗa shi da aka yi kitso aka yi da kwarkwata.

Sanusi Oscar ya yi waɗannan kalamai ne a cikin wata zantawa da ya yi da gidan rediyon Kanawa Radio da ke Kano.

A hirar, wadda wakilin mujallar Fim ya saurara, Oscar 442 wanda fitaccen daraktan fim ne, ya ce, “Mu na so kamar yadda ita tsohuwar gwamnati ta yi amfani da Hukumar Tace Finafinai ta ɓata komai, mu na so mu ma mu yi amfani da Hukumar Tace Finafinai domin mu gyara komai. Ta inda aka hau, ta nan ake sauka.

“Amma ‘problem’ ɗin da mu ke da shi, mun riga mun yi kitso da kwarkwata. Shi wannan jami’i namu, mu na yi masa kallon ungulu da kan zabo ne domin tun da ya zo bai tsaya ya kamata ya yi da ya yi na gyara ba, so ya dai biye masu maganin basir da shawara ya na ta bibiyar su, ba kuma abin da ya kamata ya yi ba, da yawan ziyarce-ziyarce da ɗaukar hotuna. Ba su ba ne abin da ya kawo shi. 

“Ba shi ne abin da ya kamata mu saka ba. Kullum mutane su na yin waƙa su na zagin sarakunan mu, su na zagin Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, su na zagin Gwamna, kuma ya zura masu idanu, ya kalle su. 

“Ko da ya ke daga ranar da aka raka shi ma mutane za su fuskanci ba shi da niyyar ya yi gyara a kan tsarin, domin mutanen da su ka raka shi waɗancan mutanen ne da mu ke ganin cewar sun yi ba daidai ba, sai mu ka gan shi da su su na murna, su na dariya a tare. To tun daga nan na san cewar akwai matsala. 

“In akwai wata shawara da zan ba wa gwamna ta Kannywood, wannan shi ne shawarar farko da zan ba wa mai girma, domin mu fara gyara wannan ɓarakar domin kar mu zo mu riƙa yin abu tufka da warwara.”

Da gidan rediyon ya tambaye shi ba ya ganin El-Mustapha cewa ya yi a zo a haɗu gaba ɗaya a yi gyara, sai ya ce, “Kai yanzu akwai wani mutumin da ka gani da aka ba shi muƙami a Nijeriya ɗan wata jam’iyya, ka ga ɗan wani jam’iyya ya raka shi? Kai a Nijeriya ina ka ga an yi wannan abin? A yau akwai ciyaman na MOPPAN na Kano State, Salisu Officer, ya kirawo shi a waya ya ce, ‘Ka na kallon yara su na zagin Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, su na zagin mai girma gwamna. Ya kamata mu tsai da wannan abin.’ Kalmar da ta fito daga bakin sa, cewa ya yi shi bai gani ba, shi bai gani ba.

“Wannan dalilin ya sa na ɗauki wani ‘clip’ da aka zagi Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso na ɗora a ‘page’ ɗi na yau, domin in bai gani ba za a gaya masa na saka.

“Kuma sabo ne aka yi? Sabo ne aka yi, bayan an naɗa tsohon gwamnan Jihar Kano shugaban jam’iyya.

“Kuma Jihar Kano aka yi wannan waƙa? A Jihar Kano, a Zoo Road, aka ci mutuncin Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. Meye amfanin mu a masana’antar Kannywood, ana zagin iyayen gidan mu, meye amfanin mu na muƙamin da aka ba mu, ana zagin iyayen gidan mu? Ka na nufin yanzu idan mu ka ƙyale wannan abin ya na ci gaba, wa mu ke taƙama da shi? Ba shi Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ba? To an zage shi, za a zagi gwamna, za a zagi kowa. Tunda shi kan shi kaɗai ne mu ke gani, shi ne allon rantsuwar mu. Yau kuma an kai ƙarshe ana yi masa, gwamnan zai samu lafiya shi ma?”

Da aka ce wa Oscar 442 wataƙila za a ce ai kun zama uwa ɗaya uba ɗaya, duk faɗi tashi, kusan tare aka riƙa ganin ku wajen yaƙin neman zaɓe, wataƙila akwai hanyar da  za a zauna a haska masa cewa kaza daidai ne, kaza ba daidai ba ne, kuma dole a gyara kaza, sai ya amsa da cewa, “Mai girma gwamna ya ce wa kwamishinonin sa ma in ba su yi daidai ba, zai cire su. Amma wannan kwamishinonin da su aka je duk 44 Local Governments, irin jin ciwo da su ke yi na nasarar zaɓe ko an faɗi zaɓe, ko an yi nasara da murnar da mutum zai yi, duk da su aka yi. Haka shi ma ɗin wannan da shi aka yi, amma fa in ka yi ba daidai ba, sai a canza ka. Ko ni na yi ba daidai ba a cire ni.”

Da Kanawa Radio ya tambaye shi idan sun ba El-Mustapha shawara don ya gyara, sai ya ce, “Bai ma neme mu ba, bai ma yarda da mu ba. Ni kawowa yanzu bai tuntuɓe ni ba. Domin abin da na gano cewa akwai matsala, da na ɗauki hoton sa na saka a soshiyal midiya ina taya shi murna, sai na ga bai ce min ya gode ba. Sai na leƙa, sai na ga ya yi wa Daso, ya yi wa Ali Nuhu, ya yi wa Maishadda, ya yi wa Maishunku, ya yi wa duk wani ɗan APC, sai na ga ni ɗan NNPP ne ɗan’uwan shi, ɗan Kwankwasiyya, bai yi min ba, sai na gano akwai matsala. To sai na gano mun yi kitso da kwarkwata, ungulu ce da kan zabuwa.”

Sai dai kuma da dama ‘yan Kannywood da sauran jama’a na yi wa Oscar kallon hassada ya ke yi wa El-Mustapha, domin a baya an yi tunanin shi za a ba muƙamin, sai kuma bai samu ba. Wannan dalilin ya sa ake kallon kamar don haka ne ya ke sukar shugaban hukumar.

Loading

Previous Post

Hannatu Umar Sani, tsohuwar jarumar Kannywood, ta rasu

Next Post

Kannywood: Abin da ya sa na tafi na dawo – Alhassan Kwalle

Related Posts

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Next Post
Malam Alhassan Kwalle

Kannywood: Abin da ya sa na tafi na dawo - Alhassan Kwalle

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!