• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Karatu yana gina tunani da halayya – marubuciyar ‘Rufaffen Duma’, Ummulkhari Sani Panisau

by MUKHTAR YAKUBU
November 1, 2025
in Marubuta
0
Karatu yana gina tunani da halayya – marubuciyar ‘Rufaffen Duma’, Ummulkhari Sani Panisau

Ummulkhari Sani Panisau da sabon littafin ta, 'Rufaffen Duma'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HARKAR rubutun littattafan Hausa da aka daɗe ana cin gajiyar ta a yanzu tana nema ta zama tarihi a ƙasar Hausa sakamakon mutuwar kasuwancin littattafai da kuma sauyin zamani da komai ya koma soshiyal midiya. Wannan ya sa a yanzu su kan su marubuta suka koma soshiyal midiya domin gudanar da aikin su, don haka a yanzu duk wani marubucin Hausa da ya shahara ko ake yayin sa za ka samu marubucin soshiyal midiya ne.

Ummulkhari Sani Panisau tana ɗaya daga cikin mata marubuta da suka yi suna a soshiyal midiya saboda salon rubutun ta na faɗakarwa da jan hankalin masu karatu. Sai dai duk da kasancewar ta fitacciyar marubuciya a soshiyal midiya, hakan bai sa ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen wallafa littafi wanda zai shiga hannun jama’a su karanta shi ko da ba su samu damar shiga soshiyal midiya ba. Ko a kwana nan ta fito da sabon littafi mai suna ‘Rufaffen Duma’ wanda a yanzu haka ya shiga kasuwa.

Za a iya cewa Ummulkhari dai ta gaji rubutu ne daga wajen mahaifiyar ta, Sadiya Garba Yakasai. Mujallar Fim ta tattauna da ita a kan rubutun ta da sabon littafin ta.

FIM: Mun ga sabon littafin da kika fitar a wannan lokacin. Shin na farko ne ko kin taɓa fitar da wani kafin shi?

UMMULKHAIRI SANI PANISAU: Tabbas, wannan littafin shi ne rubutu na farko da na yi yunƙurin wallafawa duk da cewa a baya na yi rubuce-rubuce.

Ban kai ga fitar da shi kasuwa ba. Na dai wallafa shi duba da mutanen da suka buƙaci suna son kwafi na littafin. A yanzu haka akwai masu so, su ma ana kan aikin fitar musu da shi ba da jimawa ba.

FIM: Wanne saƙo littafin yake ɗauke da shi?

UMMULKHAIRI: Daga cikin saƙonnin da labarin yake ɗauke da shi akwai yadda ‘yan siyasa suke amfani da ‘yan bangar siyasa wajen haifar da lalacewar matasa, gwagwarmayar da ɗan jarida yake yi domin tabbatar da gaskiya, yadda shigo da miyagun ƙwayoyi ya kawo lalacewar tarbiyya ga yara har ma da matasa, illar da ke ɗauke da ta’ammali da shan ƙwayoyi, da sauran su.

Ba zan iya cewa an san ni kai-tsaye ba, sai dai na san cewa na jima ina rubutu a onlayin.

FIM: An san ki a rubutun onlayin. Me ya ba ki sha’awar fitar da littafi a wannan lokacin da ake ganin kasuwancin sa ya mutu, babu ma kantinan sayar da littattafai a yanzu?

UMMULKHAIRI: Daina sayar da littattafai ba zai hana mai sha’awar buga littafi bugawa ba, saboda rubutu shi ne yake sayar da kan sa.

Zan iya buga littafi ba don na sayar ba sai domin wata rana na ɗaga na kalla na tabbatar da a lokaci kaza na yi rubutu kaza.

Zan iya buga littafi saboda shiga wata gasa.

Zan iya buga littafi saboda makaranta na manya da suke da ƙarancin gani ko kuma na nesa sun buƙaci hakan.

Kuma ba marubuta ba ne suka kashe kasuwar littafi ba. Kafin a daina sayen littafi masu aikin littafi su suka kashe kasuwar su da kan su.

Sai kuma zamani da ya ba mu damar tattarawa muka koma rubutu a yanar gizo. Shi kuma Ubangiji shi ne mai zamani, dole mu tafi da zamani a yadda ya zo. Amma har gobe ana buga littafi kuma ana saya.

FIM: Ana yi maki kallon ke ‘yar gado ce a harkar rubutu. Shin haka ne ko kuma dai kina da baiwar yin rubutun ne a kan ki?

UMMULKHAIRI: Rubutu abu ne da nake so kuma na tashi da shi a rai na. Idan da gadon rubutu zan yi to ba zan yi rubutu ba, saboda kullum mahaifiya ta Sadiya Garba Yakasai cewa take yi ba zan iya ba.

Ummulkhari Sani Panisau da mahaifiyar ta, Hajiya Sadiya Garba Yakasai riƙe da littafin ‘Rufaffen Duma’

FIM: Me labarin littafin naki ya ƙunsa?

UMMULKHARI: Na yi amfani da salon da ya haɗa labari da siyasa, inda na nuna yadda wasu mutane ke neman mulki ta hanyoyi daban-daban, har ma su hana al’umma zaman lafiya don cimma wata manufa tasu. Na kuma saka aikin jarida a ciki domin nuna rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tona gaskiya da faɗakar da jama’a.

FIM: A wanne waje ko kasuwa za a iya samun littafin naki ga masu saya?

UMMULKHAIRI: A yanzu dai masu buƙatar littafin ni suke tuntuɓa ni nake saidawa. Ana iya samu kuma ta hanyar yanar gizo Arewapen, Telegram, sannan akwai Document ɗin shi ga masu buƙatar shi a waya.

FIM: Wanne irin buri kike da shi a harkar rubutu a nan gaba?

UMMULKHARI: Buri na shi ne in zama cikin manyan marubutan da za su bar tarihi ta hanyar isar da saƙon gaskiya, kuma in kafa gidauniyar tallafa wa sabbin marubuta, musamman mata.

FIM: Ko wace irin nasara kika samu wadda ba za ki manta da ita ba?

UMMULKHAIRI: Nasarar da ba zan taɓa mantawa ba ita ce lokacin da mutane suka rinƙa kira na a kan littafin ‘Rufaffen Duma’, suna ƙarfafa mini gwiwa suna jinjina wa ƙoƙari na wajen kawo labarin duba da lokacin da muke kai a yanzu. Na samu alkairai kuma na sha addu’o’i daga wajen mutane da dama. Wannan ya sa na ji a rai na ko a iya haka na samu nasara mai girma.

Ummulkhari Sani Panisau riƙe da littafin ta na ‘Rufaffen Duma’

FIM: Wanne ƙalubale marubuta suke fuskanta?

UMMULKHAIRI: Ƙalubale mafi girma shi ne rashin tallafi da ƙarancin masu karatu masu biyan kuɗi don karanta littafi. Hasali ma in marubuci ya yi rubutun sa na kuɗi, sai an samu wanda zai fitar, wanda hakan na kashe kasuwa sosai. Marubuci yana buƙatar goyon baya, musamman wajen buga littafi da yaɗa shi.

FIM: A yanzu wanne taimako marubuta suke buƙata?

UMMULKHARI: Taimako da marubuta suke buƙata shi ne ƙarfafa ƙungiyoyin marubuta. Gwamnati da kamfanoni su rinka tallafawa wajen fitar da littattafai masu ma’ana da darussa. Sannan a kafa masana’antar karatu da wallafa ta zamani.

FIM: Menene saƙon ki na ƙarshe?

UMMULKHARI: Saƙo na na ƙarshe shi ne ina kira ga masu karatu da su ci gaba da karanta littattafai, domin karatu yana gina tunani da halayya. Kuma ina roƙon su da su goyi da bayan marubuta ta hanyar sayen littattafan su, ba kwafen su ba.

FIM: Madalla, mun gode.

UMMULKHAIRI: Ni ma na gode sosai.

Loading

Previous Post

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

Next Post

Jarumin Kannywood, Mato Yakubu ‘Malam Nata’ala’ ya kwanta dama sakamakon ciwon daji

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Jarumin Kannywood, Mato Yakubu ‘Malam Nata’ala’ ya kwanta dama sakamakon ciwon daji

Jarumin Kannywood, Mato Yakubu 'Malam Nata'ala' ya kwanta dama sakamakon ciwon daji

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!